EFCC ta bayyana yadda Ministar Jonathan ta wawuri Naira Biliyan 5 a 'yan watanni 4

EFCC ta bayyana yadda Ministar Jonathan ta wawuri Naira Biliyan 5 a 'yan watanni 4

- Hukumar EFCC ta na zargin Stellah Odua da aikata laifuffuka har 25

- Stella Oduah ta rike kujerar Minista a Gwamnatin Goodluck Jonathan

- EFCC ta na zargin kamfanin CCECC da wasu mutane 9 da laifi a kotu

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa, ta na zargin Sanata Stella Oduah da kamfanin CCECC a hannu a wata badakalar kudi.

Jaridar Premium Times ta na zargin cewa tsohuwar Ministar ta hada kai da kamfanin CCECC na kasar waje, inda aka wawuri Naira biliyan biyar a shekarar 2014.

Rahoton ya bayyana cewa an tafka wannan ta’adi ne a cikin watanni hudu, a lokacin Stella Oduah ta na rike da kujerar Ministar harkokin jiragen sama a Najeriya.

A halin yanzu ana kotu tsakanin EFCC da wadanda ake tuhuma, amma Alkali Inyang Ekwo ya daga shari’a saboda hukumar ta gaza gurfanar da wadanda ake zargi.

KU KARRANTA: 2019: Stella Oduah ta lashe zaben Sanata a Jihar Anambra

Da ta ke ofis, Stella Oduah ta ba kamfanin China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC) Nigeria Ltd wanda cibiyarsa ta na kasar Sin, kwangiloli.

EFCC ta na zargin tsohuwar Ministar da wasu mutane tara da hada-kai wajen safarar kudin sata, wadanda aka karkatar da su zuwa wani asusu domin a batar da kama.

Ana tuhumar tsohuwar Ministar da wata Gloria Odita da bude asusun Dala a wani banki, aka sulale da Naira biliyan 2.5 daga kamfanin CCECC Nigeria LTD a 2014.

Tsakanin farkon Maris zuwa karshen Mayun 2014, CCECC ya aika N868409, 349.00 zuwa wannan assusu, an kuma sake aika N500,000,000 a watan Afrilun wannan shekarar.

KU KARANTA: Diezani ta tilasta Jonathan ya sallame ni daga aiki - Stella Oduah

EFCC ta bayyana yadda Ministar Jonathan ta wawuri Naira Biliyan 5 a 'yan watanni 4
Sanata Stella Oduah Hoto: www.guardian.ng
Source: UGC

Jami’an EFCC sun bankado yadda kudi su ka rika yawo daga wannan asusu zuwa wasu akawun, ana zargin duk an samu wadannan kudi ne ta hanyar da ta saba doka.

A kan wannan ne hukumar EFCC ta ke neman kotu ta kama Oduah da mukarrabanta da laifi.

A 2014 ne shugaban kasa na wancan lokaci, Goodluck Jonathan, ya tsige Oduah bayan an zarge ta da amfani da NCAA wajen wajen sayen motocin Naira miliyan 255.

A makon da ya gabata ne ku ka ji cewa hukumar EFCC za ta gurfanar da Stella Oduah bisa zarginta da ake yi na satar kudi a lokacin tana ministar gwamnatin tarayya.

EFCC ta dade tana zargin Oduah da yin rub da ciki a kan dukiyar gwamnati a lokacin PDP.

Lauyan da ya tsaya wa EFCC, Hassan Liman, ya sanar da kotu cewa tsohuwar ministan ba ta shirya zuwa kotun ba, don haka ya bukaci alkali ya dage wannan karar.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel