Saboda kariya nace makiyaya su dinga yawo da AK47, Gwamnan Bauchi ya kare kansa
- Gwamnatin jihar Bauchi ta kara haske a kan kalaman gwamnan jihar inda yace makiyaya su dinga yawo da AK-47
- A wata takarda da hadimin Gwamna Mohammed ya fitar, ya ce ba a fahimci tsokacin da ubangidansa yayi bane da kyau
- Mukhtar Gidado ya ce Gwamna Mohammed ya sanar da hakan ne da nufin masu ruwa da tsaki su hana tabarbarewar lamurran
Gwamnatin jihar Bauchi ta kara haske a kan jawabin Gwamna Bala Mohammed inda yace makiyaya su dinga yawo da AK-47 domin baiwa kansu kariya.
A wata takarda da aka fitar a ranar Lahadi 14 ga watan Fabrairu, Mukhtar Gidado wanda babban mai baiwa gwamnan shawara ne a kafafen sada zumunta ya ce ba a fahimci tsokacin ubangidansa bane, The Punch ta wallafa.
Idan za a tuna, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bukaci makiyaya su dinga yawo da AK-47 domin shawo kan matsalar satar shanunsu da ake yi.
KU KARANTA: Sojin Najeriya sun sheke Abul-Bas da Ibn Habib, manyan kwamandojin Boko Haram
Amma a martanin da gwamnan yayi, Gidado ya ce ba a fahimce shi bane kuma ba yana nufin goyon bayan 'yan ta'addan makiyaya bane.
"Gwamnan zai so a gane cewa yana so ne ya janyo hankalin masu ruwa da tsaki da su yi kokarin hana hauhawar rikici kamar dai yadda duk wani mai kishin kasa zai yi. A kuma gujewa duk wani hari da zai iya jefa kasar nan cikin halin rikici."
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sheke Ali Bahago, wani shugaban 'yan sa kai a Katsina
A wani labari na daban, Ahmad Gumi, babban malamin addinin nan, ya ce 'yan bindiga suna tattara kudaden da suke amsa a matsayin kudaden fansa daga hannun jama'a don siyan makami mai linzami na harbo jiragen saman.
Gumi ya samu ganawa da wasu 'yan bindiga a dajin jihar Zamfara. Bayan ganawar ne ya bukaci gwamnatin tarayya ta yafe musu ta kuma taimaka musu, don sun rasa shanunsu sakamakon rikicin nan.
A tattaunawar da The Punch suka yi da Gumi, ya ce da yuwuwar ta'asar 'yan bindiga ta karu idan gwamnati bata yi wani abu ba a kai.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng