Rashin tsaro: Ku yi addu'a Ubangiji ya kawowa Najeriya sauki, Sarkin Bauchi

Rashin tsaro: Ku yi addu'a Ubangiji ya kawowa Najeriya sauki, Sarkin Bauchi

- Sarki Rilwanu Suleiman Adamu na Bauchi ya bukaci 'yan Najeriya da su koma ga Allah

- Basaraken ya yi kira ga mabiya dukkan addinai da su karkata zuwa Ubangiji a wannan lokacin

- Ya ce rashin tsaron da ya addabi kasar nan jarabawace kuma Allah ne kadai zai iya yayewa

Sarki Bauchi, Rilwanu Suleiman Adamu, yayi kira ga 'yan Najeriya da su nemi taimakon Allah domin kawo saukin rikice-rikicen da suka yi yawa a kasar nan ballantana rikicin makiyaya da manoma.

Basaraken wanda yayi wannan kiran yayin da ya karba wasu Yarabawa da suka kai masa ziyara a fadarsa da ke Bauchi, ya bukaci dukkan 'yan Najeriya na kowanne addinai da su koma ga Ubangiji a wannan lokacin jarabawar.

KU KARANTA: Muhammadu Sanusi II bai san nauyin da ke kan sarakuna ba, ya cika surutu, Ganduje

Rashin tsaro: Ku yi addu'a Ubangiji ya kawowa Najeriya dauki, Sarkin Bauchi
Rashin tsaro: Ku yi addu'a Ubangiji ya kawowa Najeriya dauki, Sarkin Bauchi. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Basaraken ya shawarci 'yan siyasa da su san abubuwan da za su dinga furtawa domin gujewa ruruta wutar rikici.

Ya yi kira ga mazauna jihar da su mutunta juna tare da rungumar zaman lafiya a tsakanin dukkan kabilu, Daily Trust ta wallafa.

Tun a baya, shugaban Yarabawa na jihar Bauchi, Tirimisiyu Adegoke, ya ce dukkan jama'arsa da ke jihar ba za su kuskure ba wurin yin karantsaye ga zaman lafiyan jihar.

KU KARANTA: Za mu yi ramuwar gayya idan aka hana makiyaya zaman kudu, Kungiyar Fulani

A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya sun halaka gagararrun kwamandoji biyu na Boko Haram, Abul-Bas da Ibn Habib a Banki, kusa da Pulka a jihar Borno kamar yadda PM News ta wallafa.

Kamar yadda aka gano, kwamandojin biyu tare da masu tsaronsu da mayaka duk an kashe su a ranar Juma'a bayan sojin Najeriya sun kai musu hari.

Abul-Bas da Ibn Habib na daga cikin manyan kwamandojin Boko Haram amma na bangaren Shekau wadanda ke ta'adi a dajin Sambisa da kewaye.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel