PTF: Sai an tashi-tsaye, Ebola ta dawo ana tsakiyar fama da annobar COVID-19

PTF: Sai an tashi-tsaye, Ebola ta dawo ana tsakiyar fama da annobar COVID-19

- Kwamitin PTF ya tabbatar Ebola ta shigo wasu kasashen Afrika

- Boss Mustapha ya ce za a sa ido domin hana cutar shigowa Najeriya

- Shugaban PTF ya na tsoron yaki da COVID-19 da Ebola a lokaci guda

Gwamnatin tarayya ta sanar da mutanen Najeriya cewa su fadaka game da wata annobar cutar Ebola da ta ke sake barkewa a kasashen makwabta.

Daily Trust ta rahoto shugaban kwamitin yaki da annobar COVID-19 watau PTF, Mista Boss Mustapha, ya na fadakar da jama’a a kan annobar.

Boss Mustapha ya jawo hankalin mutane ne a lokacin da yake magana da ‘yan jarida a Abuja.

Shugaban PTF, Boss Mustapha, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na kara sa idanu da kyau a iyakokin kasar nan bayan ganin cutar ta na dawowa.

KU KARANTA: Labarin cewa an nada ni shugaban DPR karya ce - Bashir Ahmaad

Cutar Ebola wanda aka yi a shekarun baya, ta bayyana a kasashen Afrika da ke kusanci da Najeriya, musamman a irinsu Guinea da kuma Kongo.

“Za mu cigaba da zura idanu, domin mu guji yaki da miyagun cututtuka biyu a lokaci guda.”

Mustapha ya kara da cewa: “Wannan ba aikin gwamnati ba ce kadai, sai duka ‘Yan Najeriya da sauran jama’a sun fahimci cewa akwai rawar da za su taka.”

Da yake bayanin inda aka kwana wajen yaki da annobar COVID-19, shugaban kwamitin da shugaban kasar ya kafa ya ce cutar ta hallaka mutum 1, 753.

KU KARANTA: Rikicin Oyo: Gwamnonin Jihohin Arewa sun zauna da Gwamnatin Oyo

PTF: Sai an tashi-tsaye, Ebola ta dawo ana tsakiyar fama da annobar COVID-19
Shugaban PTF, Boss Mustapha
Source: Twitter

"Zuwa ranar Lahadi, an samu mutane 146, 354 da su ka kamu, 23,408 (16%) su na jinya, an sallami 121,193 (82.8%), an kuma yi wa mutane 1,441,013 gwaji.” inji PTF.

A jiya aka ji cewa an nada Mrs Ngozi Okonjo Iweala a matsayin shugabar kungiyar WTO.

Mrs. Ngozi Okonjo-Iweala ta zama mace ta farko kuma bakar fata da ta zama shugaban kungiyar kasuwancin Duniyar bayan ta doke sauran wasu 'yan takarar.

Wa'adinta zai fara ne daga ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2021. Ana sa ran cewa tsohuwar Ministar kudin Najeriyar za ta farfado da tattalin kasashen Duniya.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel