Gwamnoni 4 sun sa labule da Gwamnan Oyo a kan harin da aka kai wa mutanen Arewa

Gwamnoni 4 sun sa labule da Gwamnan Oyo a kan harin da aka kai wa mutanen Arewa

- Gwamnonin Arewa sun tada tawaga ta musamman da ta ziyarci jihar Oyo

- Hakan na zuwa ne bayan rigima ta kaure tsakanin Hausawa da Yarbawa

- Gwamnonin za su ziyarci kasuwar Shasha, sannan za su gana da al’umma

Wasu daga cikin gwamnonin yankin Arewacin Najeriya, sun tafi Kudu, inda su ka gana da takwaransu a kan rikicin da ake fama da shi a yankin.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa gwamnonin Arewa da su ka zauna da gwamnatin jihar Oyo sun hada da gwamna Abubakar Bagudu (jihar Kebbi).

Sauran gwamnonin su ne: Dr. Abdullahi Umar Ganduje (jihar Kano), Alhaji Abubakar Sani Bello (jihar Neja), da Muhammad Bello Matawalle (jihar Zamfara).

Rahoton ya bayyana cewa an yi wannan zama ne a yammacin ranar Litinin, 15 ga watan Fubrairu, 2021.

KU KARANTA: Dole Buhari, Gwamnan Oyo su yi maganin hare-hare – Matawalle

Gwamnonin sun isa gidan gwamnatin jihar Oyo da kimanin karfe 7:00 na dare, daga nan aka jagorance su zuwa wajen Mai girma gwamna Oluseyi Makinde.

Wannan zama da aka yi a bayan labule ya na da nasaba da rikicin da ya barke a kasuwar Shasha inda Hausawa da Yarbawan jihar Oyo su ka auka wa juna da fada.

A yau Talata ne ake sa ran cewa wadannan gwamnoni za su ziyarci kasuwar Shasha domin gane wa idanunsu duk abubuwan da su ka wakana a makon da ya gabata.

Har ila yau ana sa ran gwamnonin jihohin za su yi wani zama da masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaro, da nufin kawo zaman lafiya tsakanin al’ummar yankin.

KU KARANTA: Sarakunan Yarbawa na hada kai da masu satar mutane

Gwamnoni 4 sun sa labule da Gwamnan Oyo a kan harin da aka kai wa mutanen Arewa
Gwamnoni a Ibadan Hoto: @Seyiamakinde
Asali: Twitter

Masu ba gwamnan Oyo shawara a kan harkar tsaro, Fatai Owoseni da sha’anin mutanen Arewa, Alhaji Ahmad Murtala; da wasu Sarakuna sun halarci taron na jiya.

Kafin nan sai da ku ka ji cewa tawagar Gwamnonin Arewa ta isa jihar Kaduna da nufin yin zama kan rikicin Shasha wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Bayin Allah.

Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bada sanarwar wannan taro a shafinsa na Twitter ya ce ana wannan zama ne a gidan taron nan na Arewa House.

Fadar Shugaban kasa ta kira taro inda Gwamnonin yankin su ka zauna kan kashe-kashen da aka yi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel