Hadimin Shugaba Buhari ya musanya rade-radin samun kujera mai tsoka a Ma'aikatar man fetur

Hadimin Shugaba Buhari ya musanya rade-radin samun kujera mai tsoka a Ma'aikatar man fetur

- Mai ba Shugaban kasa shawara, Bashir Ahmaad, ya yi magana a kan jita-jitar samun babbar kujera

- Bashir Ahmaad ya karyata rade-radin da ya ke yawo na cewa ya zama shugaban hukumar DPR

Mai ba shugaban kasa shawara, Bashir Ahmaad, ya musanya rade-radin da ake yi na cewa ya samu babbar kujera a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Ana jita-jitar cewa an nada Bashir Ahmaad a matsayin shugaban hukumar DPR mai kula da harkar mai, amma hadimin shugaban Najeriya ya ce ba haka ba ne.

Wata jarida ta kafar zamani ta rahoto cewa an nada Ahmaad ya shugabanci ma’aikatar a boye. Jaridar ba ta iya bada hujjar da ke gaskata rahoton da ta fitar ba.

Bashir Ahmaad wanda ya ke aiki a matsayin mai taimaka wa shugaban kasa a kafafen yada labarai na zamani ya ce bai cikin ma’aikatan hukumar DPR na kasa.

KU KARANTA: Motocin Najeriya za su kara araha

Wannan matashi ya musanya rahoto ne a shafinsa na Twitter, ya ce wani ya kawo masa gulmar rahoton bogin da ke yawo na cewa ya zama Manaja a hukumar DPR.

“Wani aboki na ya aiko mani wani labari da aka kirkira daga shafin labarai na yanar gizo cewa an yi sadaf-sadaf, an nada ni Manaja a ma’aikatar DPR ta arzikin mai.”

“Ga masu bukatar sanin gaskiya, wannan labari 100 bisa 100 karya ne. Ni ba ma’aikacin DPR ba ne.”

A wani karin bayani da ya yi a Twitter, ya kara da cewa: “Ban ma san inda ofishin DPR yake ba, abin da na sani kurum dai shi ne ofishinsu ya na Legas. Shikenan!

Hadimin Shugaba Buhari ya musanya rade-radin samun kujera mai tsoka a Ma'aikatar man fetur
Bashir Ahmaad Hoto: @Bashirahmaad
Asali: Twitter

KU KARANTA: Okorocha ya yi wa matarsa kyauta mai ban mamaki a ranar Masoya

Malam Ahmaad ya na cikin matasan da su ke rike da mukamai a gwamnatin Buhari tun 2016.

A baya kun ji cewa Kungiyar Lauyoyi na kasa watau NBA su na karar shugaba Muhammadu Buhari a kan karawa Sufeta Janar na 'yan sandan karin wa'adi.

Shugaban 'yan sandan kasar ya samu karin wa’adin watanni uku a ofis duk da ya kai shekarun ritaya.

Lauyoyin Najeriya sun saba a kan karin wa’adin da aka yi wa Mohammed Adamu, su ka ce a dokar aiki, ya kamata ya yi ritaya tun da ya shekara 35 ya na aiki.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng