Majalisar dattijai ta tsayar da lokacin tantance sabbin hafsoshin tsaro da Buhari ya nada

Majalisar dattijai ta tsayar da lokacin tantance sabbin hafsoshin tsaro da Buhari ya nada

- Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin harkokin soji a majalisar dattijai, ya ce zasu tantance sabbin hafsoshin rundunonin soji a mako mai zuwa

- A cewar Ndume, zasu tantance sabbin hafsoshin ne a wani zama na sirri da kwamitinsa zai gudanar

- A ranar Larabar da ta gabata ne shuganam majalisar dattijai, Ahmed Lawan, ya mika bukatar shugaba Buhari na neman tantance hafsoshin ga kwamitin Ndume

Shugaban kwamitin sa ido kan harkokin rundunar soji a majalisar dattijai, Sanata Ali Ndume ya ce kwamitin haɗaka na majalisar dattijan kan harkokin tsaro da suka hada da na rundunar tsaro, sojin kasa, sojin ruwa da sojin sama za su fara tantance sabbin hafsoshin tsaron Nigeria a cikin makon da zamu shiga.

Ndume ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga jaridar The Nation a Abuja.

A ranar Larabar da ta gabata, shugaban majalisar dattijan Ahmad Lawan, ya mika bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na amince da sabbin hafsoshin tsaron ga kwamitin haɗaka na majalisar dattijan da ya haɗa da kwamitin rundunar tsaro, sojin kasa, sojin sama da sojin ruwa, domin su yi kyakkyawan bincike.

KARANTA: Ba a sulhu da ƴan ta'adda: Cacar baki ta barke tsakanin El-Rufai da Sheikh Gumi

Lawan ya ba kwamitin makonni biyu da su je su yi binciken su tare da maido masa da rahoto a yayin zaman majalisar.

Majalisar dattijai ta tsayar da lokacin tantance sabbin hafsoshin tsaro da Buhari ya nada
Majalisar dattijai ta tsayar da lokacin tantance sabbin hafsoshin tsaro da Buhari ya nada
Asali: Twitter

Sabbin hafsoshin tsaron da aka naɗa su ne: Manjo Janar Lucky Eluonye Onyenuchea Irabor a matsayin shugaban rundunar tsaro; Manjo Janar Ibrahim Attahiru (Hafsan rundunar sojin kasa); Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo (Hafsan rundunar sojin ruwa); da kuma Air Vice Marshal Isiaka O. Amao (Hafsan rundunar sojin sama).

KARANTA: Reshe ya juye da mujiya: Sojoji sun dakile harin kwanton bauna tare da kashe 'yan Boko Haram 19 a Rann

Za su maye gurbin tsofaffin hafsoshin tsaron da suka hada da Janar Abayomi ( shugaban rundunar tsaro); Laftanar Janar Tukur Buratai (Hafsan rundunar sojin kasa); Vice Admiral Ibok Ete Ibas (Hafsan rundunar sojin ruwa) da Air Vice Marshal Sadique Abubakar (Hafsan rundunar sojin sama).

Yayin amsa tambayoyi, Ndume ya ce: "Bai kamata a tantance hafsoshin tsaron a bainar jama'a ba.

"Idan ka yi hakan to kamar kana nufin za ka kawo tarnaki wa tsaron kasa musamman ma idan akwai al'amuran da ke faruwa na damuwa ga tsaron kasar."

Ya ce kwamitin hadakar zai tantance sabbin hafsoshin tsaron a cikin wannan makon tunda dai makonni biyu kawai a ka ba kwamitin.

A makon da ya gabata ne Legit.ng ta rawaito cewa Muhimman bayanai na cigaba da fitowa dangane da dalilan hana cinikayya da sulallan "Crypto" a Nigeria.

Hukumar FBI ta kasar Amurka ta ankarar da gwamnatin tarayya cewa ana janye kudade daga kasashen turai tare da shigo da su Nigeria ta hanyoyin damfara.

Wata majiya ta bayyana cewa 'yan damfara na shigo da tsakanin $200m zuwa $300m zuwa Nigeria kowanne sati.

Naziru Dalha Taura Malamin makaranta ne kuma dalibi da ke sha'awar rubuce-rubuce akan dukkan al'amuran da suka shafi jiya da yau. Ya samu kusan shekaru hudu yana aiki da Legit.ng.

Ya kammala karatun digiri na farko a Jami'ar Bayero da ke Jihar Kano a bangaren ilimin kimiyyar sinadaran rayuwa da tasirinsu a jikin dan adam.

Za'a iya tuntubarsa kai tsaye a shafinsa na tuwita a @deluwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel