Sojoji sun dakile harin kwanton bauna tare da kashe 'yan Boko Haram 19 a Rann

Sojoji sun dakile harin kwanton bauna tare da kashe 'yan Boko Haram 19 a Rann

- Sojoji sun dakile harin kwanton bauna da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai musu a garin Rann

- Wata majiya ta bayyana cewa akalla mayakan kungiyar Boko Haram 19 sojoji suka kashe bayan dakile harin

- Mayakan Boko Haram sun dira garin Rann da misalin karfe 6:00 na yamma a motocinsu na yaki da babura

Rundunar sojojin Nigeria ta dakile wani harin kwanton bauna tare da kashe 'yan ta'adda 19 bayan wata zazzafar musayar wuta da mayakan kungiyar Boko Haram a garin Rann da ke yankin karamar hukumar Kala-Balge a jihar Borno.

PRNigeria ta rawaito cewa 'yan Boko Haram sun dira garin Rann da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Talata a motocinsu na yaki da babura.

'Yan ta'addar sun yi yunkurin kaddamar da harin kwanton bauna a kan tawagar rundunar soji ta uku da ke garin Rann.

KARANTA: FG: An kori ma'aikata fiye da 42 a NEMA bayan hanasu albashin shekara guda

A cewar PRNigeria, dakarun rundunar soji sun yi lambo tare da yin kamar sun janye jiki domin bawa sojojin sama damar yin ruwan wuta akan yan ta'addar.

Sojoji sun dakile harin kwanton bauna tare da kashe 'yan Boko Haram 19 a Rann
Sojoji sun dakile harin kwanton bauna tare da kashe 'yan Boko Haram 19 a Rann
Asali: Facebook

Wata majiya ta sanar da PRNigeria cewa ruwan wuta ya tilasta 'yan ta'addar neman hanya guduwa, hakan kuma ya bawa sojojin da ke kasa damar tarfa su tare da kara yi musu luguden wuta.

KARANTA: Ba a sulhu da ƴan ta'adda: El-Rufai ya maida wa Sheikh Gumi martani

"Sojoji sun lalata motocin yaki biyar da mayakan Boko Haram suka zo da su tare da mutanen da ke cikin motocin.

"Dakarun soji sun kashe da dama daga cikin 'yan ta'addar. Akwai gawarwakin mayaka da dama a wurin, an samu gawar 19 daga cikinsu jim kadan bayan lafawar luguden wuta. Akwai wasu da aka yi wa luguden wuta a hanyarsu ta guduwa," a cewar majiyar.

A baya Legit.ng ta wallafa cewa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta sanar da bullo da sabon shirin bayar da ilimi mai taken ASP (Alternate School Programme).

ASP sabon shirin gwamnatin Buhari ne da zai tabbatar da bayar da ilimi kyauta ga yara marasa galihu da basa zuwa makaranta.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa burin gwamnatinsa shine bayar da ilimi ga dukkan yaran da ke Nigeria.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel