Tambuwal: Ta hannun mata masu tallar nono 'yan bindiga ke samun miyagun kwayoyi

Tambuwal: Ta hannun mata masu tallar nono 'yan bindiga ke samun miyagun kwayoyi

- Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya karbi bakuncin wata tawagar da ta dauki alhakin yin wa'azi domin shiryar da 'yan bindiga

- A jawabin da ya gabatar yayin karbar tawagar, Tambuwal ya sanar da su cewa matsalar tu'ammali da miyagun kwayoyi na kara rura wutar rashin tsaro

- Tambuwal ya bayar da labarin da wani gwamna ya bashi dangane da abinda ya faru har ya san cewa matan Fulani na safarar miyagun kwayoyi ga 'yan ta'adda

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi ikirarin cewa matan da ke saye da sayar da nonon shanu, su ke safarar makamai wa ƴan ta'adda.

Ya yi wannan iƙirarin ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar wa'azi da shiryar da 'yan ta'adda ta Sheik Ahmad Gummi (S-GULBAR) a Sokoto, a ranar Asabar, kamar ydda Daily Trust ta rawaito.

"Wani gwamna ya taba bani wani labari. Ya shaida mun cewa ya taba kai ziyara wani kauye inda ya so ya tallafawa matan da suke kasuwanci a kauyen, inda ya same su kan hanyar su ta komawa gida dauke da nono da wasu kaya.

KARANTA: Duban kurilla: 'Yan Nigeria sun hango kurakurai biyu a jikin sabon katin APC na Tinubu

"A lokacin da ya kira su, sai wata daga cikin su ta gudu. Da ya tambayi dalilin guduwar ta sai aka shaida masa cewa ba nono ne ta dauko a kwaryarta ba, miyagun kwayoyi ne.

"Abokin nawa, ya shaida mun cewa mafi akasarin miyagun kwayoyin da yan ta'addan ke tu'ammali da su, masu tallar nono ne ke kai masu.

Tambuwal: Ta hannun mata masu tallar nono 'yan bindiga ke samun miyagun kwyoyi
Tambuwal: Ta hannun mata masu tallar nono 'yan bindiga ke samun miyagun kwyoyi
Asali: Twitter

"Da wannan dalili, ya zama wajibi Mu kawo karshen safarar miyagun kwayoyi. Idan ba haka ba za mu zo ne muna kashe maciji amma ba mu sare kansa ba," a cewar Gwamnan Sokoton.

A cewar Tambuwal, "ya zama wajibi mu rinka duba irin rawa da miyagun kwayoyi ke takawa wajen rura wutar ta'addanci."

Gwamnan ya ƙara jaddada cewa Musulunci addini ne na zaman lafiya, kuma nusar da mutane hakan zai fargar da masu garkuwa da mutane, Boko Haram da sauran yan ta'addan kan munanan halayen su.

KARANTA: Fahimta Fuska: Ganduje ya shirya muhawara tsakanin Abduljabar da manyan Malaman Kano

Ya kuma yabawa kokarin tawagar S-GULBAR na wannan babban aikin da ta sanya a gabanta na wa'azantar da yan ta'adda, tare da yin alkawarin tallafa masu.

Tun farko shugaban wannan tawagar ta S-GULBAR, Sheikh Gumi, ya yi nuni da cewa ana rikon sakainar kashi ga matsalar tsaro da ta ke addabar yankin Arewa, kuma rashin hadin kan shuwagabanni da mabiyansu zai taimaka ne kawai wajen kara tabarbarewar matsalar.

Haka zalika tawagar S-GULBAR ta ziyarci Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar a fadarsa da ke Sokoto.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya kai ziyara jihar Sokoto don jajantawa takwaransa, gwamna Aminu Waziri Tambuwal, bisa mummunar gobarar kasuwar da ta faru ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.

Yayin ziyarar, gwamna Wike ya bawa gwamnatin jihar Sokoto gudunmuwar milyan dari biyar (N500,000,000) domin sake gina kasuwar.

Hakazalika, Wike ya kai ziyara fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubuakar Sa'ad.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel