Kona coci da sansanin sojoji a Nigeria: Ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kai hari

Kona coci da sansanin sojoji a Nigeria: Ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kai hari

- Mayakan ISWAP sun dauki alhakin kona coci da sansanin soji a jihar Borno

- A cewar kungiyar, mayakanta sun kaddamar da harin ne a ranar 10 ga watan Fabrairu a garin Askira

- Ta kuma bayyana cewa sun kashe dakarun sojoji guda uku a harin

Rahotanni sun kawo cewa kungiyar ta’addanci ta ISWAP ta dauki alhakin kai harin tare da kona wani coci da sansanin sojoji a jihar Borno.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa a wata sanarwa da ta fitar a shafin sada zumunta,Kungiyar ta ISWAP ta ce mayakanta sun kai mamaya garin Askira a Askira-Uba a ranar 10 ga watan Fabrairu, inda suka kashe sojoji uku.

KU KARANTA KUMA: Sabunta rijistar jam'iyyar APC: Abdul'aziz Yari ya caccaki ra'ayin Tinubu

Kona coci da sansanin sojoji a Nigeria: Ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kai hari
Kona coci da sansanin sojoji a Nigeria: Ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kai hari Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Kungiyar ta dauki alhakin rike ikon harin tsawon sa'o'i sannan kuma a lokacin ne yan ta’addan suka kona wani coci da sansanin sojojin.

Mun ji cewa Kungiyar ta ɗauki alhakin jerin hare-hare a yan kwanakin nan a arewa maso yammacin kasar, musamman kan sojoji.

A gefe guda, mun ji cewa bayanan da jami’an tsaro su ke samu a Najeriya ya nuna cewa ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun kafa wasu sababbin sansanoni a Arewa maso gabas.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar 11 ga watan Fubrairu, 2021, ta tabbatar da wannan lamari. Rahoton ya ce ‘yan ta’addan wanda su ka shafe shekara da shekaru su na ta barna a yankin sun samu wasu mafaka inda za su rika boye wa jami’an tsaro.

Majiyar jami’an tsaro ta kuma bayyana cewa akwai yiwuwar ‘yan ta’addan sun tare a wasu garuruwan Yobe da su ka hada da Tarmuwa da Yunusari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel