Rikici ya barke tsakanin Makiyaya da Amotekun a Ondo, mutum 2 sun hallaka

Rikici ya barke tsakanin Makiyaya da Amotekun a Ondo, mutum 2 sun hallaka

- Jami'in Amotekun, Manomi, da motar Amotekun sun hallaka a wani rikici

- Ana zargin makiyaya da tayar da tarzoma a jihar Ondo ranar Alhamis

- Gwamnatin jihar ta umurnin makiyaya su fita daga dazukan jihar gaba daya

Akalla mutane biyu sun rasa rayukansu ranar Alhamis a rikicin da ya barke tsakanin jami'an hukumar Amotekun da wasu Fulani Makiyaya a jihar Ondo.

Premium Times ta ruwaito cewa wannan rikici ya auku ne a Ago Sanusi, hanyar Uta, karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

Majiyoyi sun bayyana cewa gabanin rikicin, makiyayan sun samu matsala da manoma kuma hakan ya sa aka kira jami'an Amotekun.

A cewar majiyar, yayinda jami'an Amotekun suka isa wajen, makiyayan suka bude musu wuta. Hakan ya yi sanadiyar mutuwar wani manomi da dan banga.

"Wani manomi da dan bangan Amotekun sun rasa rayukansu sakamakon harbin da makiyaya sukayi musu a kai," Supo Ojo, wani mazauni ya bayyana.

Yayinda aka tuntubi Kwamandan Amotekun, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da labarin.

"Wasu manoma sun kira Amotekun jiya cewa makiyaya sun kai musu hari kuma jami'anmu suka je wajen don kwantar da kuran. Wani dan banga da manomi sun rasa rayukansu a rikicin," yace.

KU KARANTA: Rashin tsaro: An maka Buhari da Makinde a kotu kan rikicin makiyaya a Oyo

Rikici ya barke tsakanin Makiyaya da Amotekun a Ondo, mutum 2 sun hallaka
Rikici ya barke tsakanin Makiyaya da Amotekun a Ondo, mutum 2 sun hallaka
Asali: Facebook

KU KARANTA: Disamba 2020: Kason da kowani bangare ya kwashe daga N601.11bn na kudaden da FG ke rabawa duk wata

A bangare guda, biyo bayan hauhawar matsalolin tsaro a kasar, Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) a ranar Juma’a, 12 ga watan Fabrairu, ta zargi wasu dattawan Yarbawa da kokarin tayar da rikici da haifar da fargaba a tsakanin mutane.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa kungiyar wacce ta yi zargin a wata wasika da ta rubuta wa Majalisar Dinkin Duniya ta lura cewa an yi hakan ne don haifar da rikici a tsakanin kungiyoyi da yankuna.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed, kakakin kungiyar NEF, ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar barazana daga mutane, suna kamun kafa da kasashen duniya, don haifar da rikici a cikin kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel