Wani bawan Allah ya tsinci kansa a kotu kan lakada wa malamin dansa dukan tsiya

Wani bawan Allah ya tsinci kansa a kotu kan lakada wa malamin dansa dukan tsiya

- Wani uba ya tsinci kansa a gaban kotu sakam,akan zarginsa da ake yi da cin zarafin wani malamin dansa

- An tattaro cewa uban ya lakada wa malamin dan nasa duka a harabar makarantarsu saboda ya tsawata wa yaron

- A halin da ake ciki dai alkalin kotun da ke sauraron shari'ar ya bayar da belinsa a kan kudi naira miliyan daya

Hukumar yan sanda a jihar Osun ta gurfanar da mahaifin wani dalibin Kwalejin Oduduwa, Ile-Ife, jihar Osun mai suna Adeyeni Adeyeye bisa zargin lakada wa malamin dansa, Mista Sanusi Ademola duka a makarantar.

Ana zargin Adeyeye, wanda aka gurfanar a kotun Majistare da ke Ile-Ife, da cin zarafi da dukan malamin wanda ya ladabtar da dan nasa bayan ya yi rashin ji.

Mai gabatar da kara, ASP Abdullahi Emmanuel, ya fadawa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 1 ga Fabrairu, 2021, da misalin karfe 10:30 na safe a harabar makarantar.

Wani bawan Allah ya tsinci kansa a kotu kan lakada wa malamin dansa dukan tsiya
Wani bawan Allah ya tsinci kansa a kotu kan lakada wa malamin dansa dukan tsiya Hoto: @THISDAYLIVE
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: Kotu ta tsige shugaban PDP da sauran shugabannin jam’iyyar a Ebonyi

Ya kara da cewa wanda ake zargin ya yiwa malamin duka ba bisa ka'ida ba ta hanyar naushinsa da kuma yayyaga masa riga, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Har ila yau ASP Emmanuel ya ce wanda ake tuhumar ya gudanar da kansa a wani yanayi da ka iya haifar da rashin zaman lafiya a cikin jama'a ta hanyar kai mamaya makarantar dan nasa tare da 'yan daba sannan suka ci zarafin malamin.

Ya ce laifin da wanda ake zargin ya aikata ya sabawa sashi na 249 (d), 351, 383, 390 (9), 451 da 516 na kundin laifuka, Cap 32, na dokar Osun, 2002.

Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin sannan lauyarsa, Oluwatosin Ademola, ta nemi a bada belinsa.

Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun A. A. Adebayo ya ba da belin a kan kudi naira miliyan 1 sannan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 3 ga watan Maris.

A wani labari na daban, wata kotun majistare da ke zama a Sokoto ta kama wasu matasa da laifin yada bidiyon tsiraicin wata yarinya a kafafen sada zumuntar zamani.

Wadanda ake zargin sune wani Aminu Tafida, da mai bada shawara na musamman ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Umar Abubakar da Mas'ud Gidado.

KU KARANTA KUMA: An yanke wa wani barawon janareto daurin watanni 3 a gidan yari

Amma kuma wanda ake zargi na hudu mai suna Aliyu Shehu kangiwa an wanke shi saboda bashi da wata alaka da wannan laifin, Daily Trust ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel