Ban taɓa yin addu'ar Allah yasa in zama gwamna ba, in ji Seyi Makinde
- Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo ya ce bai taba yin addu'ar Allah yasa ya zama gwamna ba
- Makinde ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi lokacin da ya ke tarbar mambobin FIBAN da BCOS a gidan gwamnati
- Mambobin kungiyoyin biyu sun ziyarci gwamnan ne domin neman ya saka baki kan wasu matsaloli da suke fuskanta
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, a ranar Alhamis ya ce bai yi addu'ar ya zama gwamna ba a 2019, inda ya ce kawai shi kawai fatansa shine Allah ya zartar da ikonsa a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Makinde ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tarbar mambobin Kungiyar masu watsa labarai masu zaman kansu, FIBAN, daga Kungiyar masu watsa labarai na jihar Oyo, BCOS, a gidan gwamnati da ke Agodi, Ibadan.
Gwamnan ya yi alkawarin zai duba batun sallamar wasu mambobin kungiyar da aka yi daga aiki inda ya ce gwamnatinsa ba za ta rika rufa-rufa ba kuma za ta yi tafiya tare da kowa.
DUBA WANNAN: Jiragen yakin NAF sun sake halaka yan bindiga masu yawa a Kaduna
Ya kuma yi alkawarin saka baki kan matsalolin da ke tsakanin mambobin BCOS da FIBAN cikin makonni hudu.
"Da na ke addu'a a game da zaben 2019, ban yi addu'ar Allah yasa in zama gwamna ba, ni dai addu'ar da na yi shine Allah ya zartar da ikonsa a Jihar Oyo. Don haka, na san cewa kadarar Allah ne, Zai kawo wadanda za su tabbatar da abinda ya kaddara, daya daga cikinsu shine Sanata Monsurat Sunmonu.
KU KARANTA: Tsohon gwamnan Zamfara, Yerima, ya gurfana gaban kwamiti kan zargin 'azabtar da ɗan kasuwa'
"Yanzu na fara jin korafin ku. Idan da na san wannan shine abinda za mu tattauna, da na tuntubi Prince Dotun Oyelade ya zo taron. Ina maimaitawa, ban san da wannan matsalar ba. Dukkan mu muna kuskure, Allah ne kadai baya kuskure," wani sashi cikin jawabin Makinde.
A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.
Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.
Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya tuntuɓarsa kai tsaye a shafinsa na Twitter @ameeynu
Asali: Legit.ng