An tura makasa sun bindige mutum 3 har lahira wurin taron jin ra'ayin mutane

An tura makasa sun bindige mutum 3 har lahira wurin taron jin ra'ayin mutane

- Wasu makasa su biyar sun halaka mutane uku a garin Nkpor a jihar Anambra

- Makasan sun shigo wurin taron jin ra'ayin mutane ne suka tafi kai tsaye suka harbe su

- Rundunar yan sandan jihar ta bakin kakakinta Mohammed Haruna ta tabbatar da lamarin

'Yan bindiga a ranar Laraba sun halaka mutane uku a garin Nkpor da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambara.

Premium Times ta ruwaito cewa wasu yan bindigan kimanin su biyar ne suka bi wadanda suka riga mu gidan gaskiyar zuwa wani wurin da ake taron jin ra'ayin mutane.

An tura makasa sun bindige mutum 3 har lahira wurin taron jin ra'ayin mutane
An tura makasa sun bindige mutum 3 har lahira wurin taron jin ra'ayin mutane. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

An tattaro cewa mutane ukun masu dauke da bindigun, da isarsu wurin taron sun tafi kai tsare wurin mutane ukun suka bindige su daga kusa.

Lamarin ya janyo turereniya a yayin da mutane ke kokarin tsira da kansu.

DUBA WANNAN: 'Yan tawayen Houthi sun kai hari sun ƙona jirgin saman kasar Saudiyya

"Abin da ya faru yau da rana ya bawa kowa mamaki kamar yadda kake gani kowa ya fita hayyacinsa. Makassan sun tsara harinsu sosai duba da yadda suka yi nasarar kashe dukkan mutum ukun a suke nema," in ji wani shaidan gani da ido.

"Gawarwakinsu na nan a kwance a wurin kuma babu wanda ya iya kusantarsu ko yan sanda har yanzu ba su iso ba," ya kara da cewa.

Shaidan ya ce biyu cikin wadanda aka kashe yan garin ne yayin da daya kuma daga makwabta ya zo.

KU KARANTA: Saki: Mata ta mayarwa miji sadakin N28,000 da ya biya yayin aurenta shekaru 7 da suka shude

Kakakin yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da kisar.

Ya bada sunayen mutane ukun da aka halaka kamar haka, Izuchukwu Idemili, 32, Chidi Oforma, 31, yan garin Nkpor da Bongo Muoghalu, 45, daga Umouji.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164