Bidiyon fusataccen saurayi yana kwace kayan kallo da ya siyawa budurwarsa bayan sun bata

Bidiyon fusataccen saurayi yana kwace kayan kallo da ya siyawa budurwarsa bayan sun bata

- Bidiyon fusataccen saurayi yana kwace talabijin dinsa na bango da dikodarsa daga hannun budurwa ya janyo cece-kuce

- Kamar yadda bidiyon ya bayyana, an ga budurwar tana rokon saurayin amma yayi mirsisi ya kwace kayan kallon

- An gano cewa ya siya mata ne lokacin suna soyayya amma sai ya yanke shawarar kwace kayansa bayan sun bata

A wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani, an ga wani mutum yana karbar talabijin na bango tare dekoda da ya siyawa budurwar shi.

An gano cewa saurayin ya yanke hukuncin kwace kayansa ne bayan sun rabu a soyayyar, The Nation ta ruwaito.

A bidiyon mai kayyadaddun dakika, an ga yadda matashin ya fizge talabijin din sa na bango tare da dikoda da ya siyawa budurwarsa yayin da suke soyayya.

KU KARANTA: Muna da sabbin dabarun yakar ta'addanci da 'yan bindiga a kasar nan, Osinbajo

Bidiyon fusataccen saurayi yana kwace kayan kallo da ya siyawa budurwarsa bayan sun bata
Bidiyon fusataccen saurayi yana kwace kayan kallo da ya siyawa budurwarsa bayan sun bata. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Matashin wanda ya ki girgiza da duk rokonsa da tsohuwar budurwarsa ke yi, yayi gaba da kayan kallonsa babu ko waiwaye.

Wannan bidiyon ya janyo cece-kuce mai tarin yawa daga wurin samari da 'yan mata. Wasu na ganin bai kyauta ba yayin da wasu ke ganin yayi daidai da ya aikata hakan.

KU KARANTA: Gwamnatin Bauchi ta sauya sunan jami'ar jihar zuwa jami'ar Sa'adu Zungur

A wani labari na daban, Abduljabar Nasir Kabara, babban malamin da gwamnatin Kano ta haramtawa wa'azi ya maka gwamnatin jihar Kotu a kan tsaresa da tayi ba bisa ka'ida ba.

Gwamnatin Kano ta hana Kabara wa'azi a ranar 4 ga watan Fabrairun 2021 a kan zarginsa da wa'azi da zai iya tada zaune tsaye, The Cable ta wallafa.

A ranar 7 ga watan Fabrairu, gwamnatin jihar ta amince da mukabala tsakanin Sheikh Kabara da sauran malaman addini a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: