Mata karkatar da hankali suke yi, Lauyan da yayi soyayya da mata fiye da 100

Mata karkatar da hankali suke yi, Lauyan da yayi soyayya da mata fiye da 100

- Wani lauya ya yi wata wallafa a Twitter wacce jama'a da yawa suka yi ta na'am da ita

- A cewarsa kada namiji ya kuskura ya fara kula mata har sai ya kai daukakar da yake burin samu

- Ya ce ya yi nadamar bata lokacinsa akan mata, da zama yayi ya gina rayuwarsa da yafi masa

Wani mutum mai amfani da suna ActuateCoaching ya bayar da wata shawara wacce mutane da dama suka yi na'am a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Kamar yadda mutumin wanda lauya ne kuma dan kasuwa ya wallafa, mata suna kawar da hankalin mutum daga gina kanshi.

A cewarsa, da yanzu ya tara arziki mai tarin yawa idan ba saboda bata masa lokaci da mata suka dinga yi ba.

Kamar yadda ya wallafa: "Na yi soyayya da mata akalla guda 100, masu shekaru 18-36 a cikin shekaru 25.

Mata karkatar da hankali suke yi, Lauyan da yayi soyayya da mata fiye da 100
Mata karkatar da hankali suke yi, Lauyan da yayi soyayya da mata fiye da 100. Hoto daga @ActuateCoaching
Asali: Twitter

"Idan na duba shekarun da suka shude sai in yi ta nadama, dama nayi aiki akan kaina. Da yanzu na tara kudade da sana'o'i. Gaskiya mata suna da dauke hankalin mutum."

KU KARANTA: Hotunan Auwalun Daudawa tare da mukarrabansu suna mika makamansu tare da tuba

A wani labarai na daban, yayin da kowanne dan siyasa yake shiri akan zaben shugaban kasa na 2023, jam'iyyar APC ba a barta a baya ba, sai dai alamun nasara suna ta harararta don yanzu haka gwamnoni 4 na jam'iyyar PDP sun shirya tsaf akan sauya shekarsu zuwa APC.

A ranar Litinin ne aka samu labarin yadda tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya lallaba har babban birnin tarayya, Abuja don tattaunawa da shugaban rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni da gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.

KU KARANTA: Bidiyo: Dan ka ne kuma ba zan taba yin gwajin DNA ba, Matar aure ga mijinta

Wani mai fadi a ji na jam'iyyar APC ya sanar da Punch cewa gaskiya ne batun zuwan Fani-Kayode wurin shugabannin jam'iyya, duk da dai tsohon ministan bai riga ya fadi wata magana ba tukunna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: