Majalisa ta tabbatar da shugabanin AMCON da NDIC da Buhari ya naɗa

Majalisa ta tabbatar da shugabanin AMCON da NDIC da Buhari ya naɗa

- Majalisar Dattawar Nigeria ta tabbatar da shugabannin hukumomin AMCON da NDIC

- Majalisar ta amince da nadinsu ne bayan kwamitinta na Bankuna, Inshora da wasu hukumomin kudade sun tantance su

- Shugaban kwamitin Bankuna da Inshora, Uba Sani, ya lissafa wasu nasarori da shugaban na AMCON ya samu a wa'adinsa na farko

Majalisar Dattawa a ranar Laraba ta tabbatar da nadin Ahmed Kuru da Bello Hassan a matsayin shugabannin Hukumar Kula da Kadarori ta Kasa da Hukumar Inshora, AMCON, da Hukumar NDIC kasa kamar yadda aka jero su.

Tabbatarwa na zuwa ne bayan nazarin kan rahotannin kwamitin majalisa kan bankuna da inshora da wasu hukumomin hada-hadar kudade, Premimum Times ta ruwaito.

Majalisa ta tabbatar da shugabanin AMCON da NDIC da Buhari ya naɗa
Majalisa ta tabbatar da shugabanin AMCON da NDIC da Buhari ya naɗa. Hoto: Premium Times
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan Zamfara, Yerima, ya gurfana gaban kwamiti kan zargin 'azabtar da ɗan kasuwa'

Kazalika, an tabbatar da Ebelechukwu Uneze a matsayin shugaban AMCON da Muhammad Ibrahim a matsayin shugaban hukumar Nigeria ta Inshora.

Shugaban kwamitin Bankuna, Inshora da sauran hukumomin hada-hadar kudade na majalisar, Uba Sani (APC-Kaduna Central) yayin jawabinsa ya ce an tabbatar da Mista Kuru a matsayin shugaban AMCON a 2015.

KU KARANTA: 'Yan tawayen Houthi sun kai hari sun ƙona jirgin saman kasar Saudiyya

Ya kara da cewa an samu cigaba sosai a hukumar da sauya sauye da suka inganta aiki a wa'adinsa na farko saboda sabbin tsare tsare da ya rika kawowa.

Har wa yau, 'karkashin jagorancinsa, AMCON ta yi hadin gwiwa da masu saka hannun jari da kuma bullo da aiwatar da tsarin kula da kadarori, AMP, domin taimakawa wurin warware kananan basusuka wanda hakan ya samar da ayyuka fiye da 3000.'

Ya kuma lissafa wasu ayyukan da tsare tsare da hukumar ta yi karkashin jagorancinsa.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel