Bidiyo: Dan ka ne kuma ba zan taba yin gwajin DNA ba, Matar aure ga mijinta

Bidiyo: Dan ka ne kuma ba zan taba yin gwajin DNA ba, Matar aure ga mijinta

- Wata mata ta shayar da kowa mamaki a gaban masu rajin kare hakkin bil'adama inda tayi ikirarin cewa tabbas mijinta ne mahaifin danta

- Sai dai ta lashi takobin cewa ba za ta taba yarda suje a yi musu gwajin asibiti na DNA ba don tabbatar da yaron dan shekara 7 nashi ne ko akasin haka

- Duk da mutumin ya ja ta har wurin masu rajin kare hakkin bil'adama, inda ya bukaci lallai sai sun je an tabbatar masa don kawar da kokwanto

Wata mata ta daka tsalle gaban masu rajin kare hakkin bil'adama, bayan mijinta ya takura mata da cewa sai sun je an yi musu gwajin asibiti na DNA don ya samu tabbaci idan shine asalin mahaifin danta.

Duk da ya kai kararta har wurin masu rajin kare hakkin bil'adama, ta rantse ta maya, inda tace tabbas mahaifinsa ne shi amma ba sai an yi gwajin asibiti ba.

Ta ce tabbas shine mahaifin danta, amma babu wanda zai kai mata da asibiti don yin wannan gwaji na DNA, The Nation ta wallafa.

KU KARANTA: Son komawa wasa Turai domin gogayya da manyan 'zakaru' yasa na bar Al Nassr, Ahmed Musa

Bidiyo: Dan ka ne kuma ba zan taba yin gwajin DNA ba, Matar aure ga mijinta
Bidiyo: Dan ka ne kuma ba zan taba yin gwajin DNA ba, Matar aure ga mijinta. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabunta rijista a APC: Bata-gari sun aika da shugaban APC lahira a jihar Binuwai

A wani labari na daban, kotun jihar Legas ta laifuka na musamman dake Ikeja ta yanke wa faston Living Faith Church wacce aka fi sani da Winner's Chapel, Afolabi Samuel, shekaru 3 a gidan gyaran hali bisa satar $90,000 da N4,500,000 wanda 'yan coci suka hada karfi da karfe suka tara.

EFCC ta gabatar da Samuel wanda shine akawu kuma ma'ajin cocin gaban alkali Mojisola Dada bisa laifuka biyu, almundahana da sata.

Kamar yadda EFCC ta gabatar, faston da wata Blessing Kolawole, wacce take aiki a jami'ar Covenant, sun hada kulle-kullen satar dukiyar kuma sun sake a aljihunansu don amfaninsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel