Daga karshe, kungiyar kasuwancin duniya ta amince da zabin Buhari, Ngozi Okonjo Iweala
- Shugaba Buhari ya zabi Ngonzi Iweala matsayin wacce zata wakilci Najeriya a zaben shugabancin babban kungiyar kasuwanci a duniya
- Kasar Masar ta nuna rashin amincewarta da zabin shugaban Najeriya
- Kungiyar WTO ta raba gardama tsakanin Najeriya da Masar
Kungiyar kasuwancin duniya WTO ta amince da tsohuwar ministar kudin Najeriya, Ngozi Okonjo Iweala matsayin daya daga cikin yan takaran kujerar shugabancin kungiyar, The Cable ta ruwaito.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo inda tace: "Kasar Najeriya a ranar 9 ga Yuni 2020 ta zabi Dr Ngozi Okonjo Iweala matsayin wacce za tayi takarar kujeran shugaban WTO domin maye gurbin shugaban na yanzu, Mr Roberto Azevedo, wanda ya sanar da cewa zai sauka a ranar 31 ga Agusta, 2020."
KU KARANTA: Sojoji 45 sun bace, 6 sun mutu yayinda yan Boko Haram suka kai hari
Za ku tuna cewa ya shugaba Muhammadu Buhari ya zabi Ngozi Okonjo Iweala matsayin wacce za ta wakilci Najeriya a zaben shugabancin kungiyar.
Amma kasar Masar ta nuna rashin amincewarta da hakan saboda daya daga cikin yan takaran dan kasan Masar ne.
Kasar Misra ta bukaci a soke takarar Ngozi Okonjo-Iweala na kujerar shugabar kungiyar saboda kundin dokoki ya nuna cewa zaben sabon dan takarar da Najeriya tayi "ya sabawa hukuncin da majalisar zartarwa ta yanke."
Ta ce tun watanni biyar da suka wuce, 30 ga watan Nuwamba, 2019, aka bukaci kasashe su aika sunayen yan takarar kujerar amma sai yanzu Buhari ya kawo sabon suna.
Amma ranar Talata, WTO ta ce za'a iya sauya sunaye har zuwa ranar 8 ga Yuli, 2020.
WTO tace: "Bisa ga jadawalin da shugaban majalisa, David Walker, ya sanar, za'a rufe karban sunaye ranar 8 ga Yuli 2020."
Legit.ng Hausa ta kawo rahoton cewa ranar Alhamis cewa shugaba Muhammadu Buhari ya janye takarar Yonov Frederick Agah, kuma ya maye shi da Ngozi Okonjo Iweala matsayin wacce za tayi takarar kujerar shugabar WTO.
Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng