Auwalu Daudawa: Abin da yasa na mika bindigu na 20 ga gwamnatin Zamfara

Auwalu Daudawa: Abin da yasa na mika bindigu na 20 ga gwamnatin Zamfara

- Shugaban yan bindiga a Zamfara, Auwalu Daudawa ya bayyana dalilin da yasa ya mika wuya ga gwamnati

- Daudawa ya ce ya gano cewa hare-haren bata da amfani kuma babu riba a cikin harkar

- Daudawa ya kuma ce wasu sauran yan bindigan za su bi sahunsa su mika wuya ga hukumomin tsaro

Babban kwamandan yan bindiga a Zamfara mai suna Auwalu Daudawa ya ce ya amince ya mika bindigunsa ne bayan ya gano kai hare-hare babu riba kuma bata da amfani, Daily trust ta ruwaito.

Daudawa na daya daga cikin wadanda ke jagorantar yan bindiga da ke dajin Dumburum a karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Auwalu Daudawa: Abin da yasa na mika bindigu na 20 ga gwamnatin Zamfara
Auwalu Daudawa: Abin da yasa na mika bindigu na 20 ga gwamnatin Zamfara. hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Yan kungiyarsa sun dade suna kai hare-hare a hanyar Zurmi - Gidan Jaja da Jibia.

DUBA WANNAN: Hotunan wani da aka cafke yana fashi sanye da kayan Civil Defence

Daudadawa ya sanar da hakan ne a ranar Talata a hedkwatar yan sanda da ke jihar Zamfara a Gusau, babban birnin jihar.

Ya ce ya yi imanin cewa wasu yan bindigan a dazukan Zamfara suma za su bi sahunsa su mika wuya domin dama suna neman irin wannan damar.

"Yan banga da ake fi sani da 'yan sakai suna matsa mana.

"Hakan ne yasa muka dauki makamai amma duk da hakan ba su dena matsa mana ba.

KU KARANTA: An nada Mohammed Yerima a matsayin sabon kakakin sojojin Nigeria

"Idan yan sakai (yan banga) suka cigaba da kashe fulani a kasuwanni da wasu wurare ba tare da shari'a ba ina baka tabbacin ba za a taba samun zaman lafiya ba.

"Amma mun goda wa Allah saboda shiryar da mu kan hanya madaidaiciya," in ji shi.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel