Ku dawo gida idan sun koraku, kungiyar dattawan Arewa ga Fulani Makiyaya

Ku dawo gida idan sun koraku, kungiyar dattawan Arewa ga Fulani Makiyaya

- An yi kira ga Fulanu Makiyaya su koma gida Arewacin Najeriya daga Kudu

- Kungiyar dattawan Arewa NEF ce ta bukaci makiyayan da haka

- Garuruwa da dama a kudancin Najeriya na kira ga Fulani Makiyaya su bar musu yanki sakamkon hare-hare da sace-sacen mutane

Kungiyar Makiyayan Arewa (NEF) ta bayyanawa al'ummar Fulani dake kudancin Najeriya su dawo gida idan ana koransu daga inda suka zaune.

Hakazalika Kungiyar NEF ta yi kiraga gwamnonin Arewa su shirya karban Fulanin dake shirin dawowa gida daga kudu.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa wannan na kunshe cikin jawabind da kakakin kungiyar dattawan, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya saki.

Wani sashen jawabin yace: "Idan mutanen wani sashe a kasar nan sun lashi takobin koran Fulani daga yankunansu, kungiyar na bada shawara kawai su koma Arewa."

"Gwamnonin Arewa su gaggauta shirin tarban Fulanin da aka kora daga kudu karfi da yaji."

DUBA NAN: Idan aka rage farashin mai, za'ayi wahalar mai kwanan nan, Ministan Mai

Ku dawo gida idan sun koraku, kungiyar dattawan Arewa ga Fulani Makiyaya
Ku dawo gida idan sun koraku, kungiyar dattawan Arewa ga Fulani Makiyaya
Asali: UGC

KU DUBA: Hukumar Hisbah ta damke kiret din giya 260 a jihar Bauchi

A bangare guda, Mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Adeyemo Igboho, ana zarginsa da kai hari wata rugar Fulani dake garin Igua, karamar hukumar Yewa ta Arewa a jihar Ogun, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar makiyaya Miyetti Allah (MACBAN), na jihar Ogun, Alhaji Abubakar Dende, ya bayyanawa manema labarai cewa yanzu haka yaran Sunday Igboho sun banka wuta gidan Sarkin Fulanin Igua, Alhaji Adamu Oloru.

"Sun kona gidajen dake garin da na Sarkin Fulani, Alhaji Adamu Oloru, dake Igua da yamman nan (Litinin)," ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng