Sheikh AbdulJabbar: Jama'atu Nasril Islam ta jinjinawa Ganduje da Malaman jihar Kano
- Kungiyoyin addinin Musulunci a fadin Najeriya na cigaba da jinjinawa Ganduje
- Gwamnatin Kano ta dakatad da Sheik Abdul Jabbar Nasir Kabara daga wa'azi da tarurruka
- Malaman jihar Kano na zarginsa da sukan Sahabban manzon Allah (SAW)
Kungiyar Jama'atu nasril Islam JNI, karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ta jinjinawa gwamnatin jihar Kano kan dakatad da Sheikh AbdulJabbar Nasir Kabara.
Sakataren Jama'atu, Dakta Khalid Abubakar Aliyu, a jawabin da yace, "Karnin sahabbai shine mafi Alkhairi saboda haka duk wanda yayi kokarin zaginsu ko cin mutuncinsu na kokarin fito-na-fito ne da Musulmman duniya gaba daya."
"Saboda haka, muna Alla-wadai da Abdul Jabbar na Kano da abubuwan da yake fadi."
"Wannan cin mutunci ne karara ga Manzon Allah (SAW) kuma ba zamu taba lamuntan haka be."
"Hakazalika, Jama’atu Nasril Islam na jinjinawa gwamnatin jihar Kano kan matakin da ta dauka na gaggawa wajen dakatad da wa'azuzzukan AbdulJabbar kafin a kammala bincike kan tuhumar da ake masa."
Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta bayyana irin rawan ganin da Zauren Malaman jihar Kano ya taka wajen dakile kalaman da Abdul Jabbar da kuma janyo hankalin gwamnati.
KU DUBA: Fulani Makiyayan dake kudancin Najeriya sun fara komawa jihar Kano, Miyetti Allah
KU KARANTA: Kungiyoyin Arewa suna marawa Gumi baya kan samar da filayen kiwo ta kasa
Kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana ainahin dalilan da suka sa ya dakatar da Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara daga yin wa’azi da kuma bayar da umurnin rufe masallacinsa a Kano, tare da yin watsi da ikirarin malamin na cewa lamarin siyasa ce.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta bari mutum daya ya jawo rashin zaman lafiya ba a jihar.
“Muna ta kallon ayyukansa a tsanaki. Jami’an tsaro na taka-tsantsan da abunda yake yi sosai kuma kun ga mun dauki mataki," Ganduje yace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng