Za mu dauko Sojin haya daga Chadi da Kamaru don kawar da yan Boko Haram, COAS

Za mu dauko Sojin haya daga Chadi da Kamaru don kawar da yan Boko Haram, COAS

- Sabon shugaban Sojin kasa ya bayyana salon da zai yi amfani da shi wajen yakan Boko Haram

- Da alamun ya amince da shawaran dauko sojin kasashen wajen musamman Chadi da Kamaru

- Har yanzu majalisar dattawa bata tabbatar da sabbin hafsoshin tsaron ba

Shugaban Hafsoshin Sojin Kasa, Ibrahim Attahiru, ya bayyana cewa Najeriya za ta dauko sojin haya daga kasar Chadi da Kamaru domin kawo karshen yan ta'addan Boko Haram a kasar nan.

Yayin jawabi ga rundunar Supercamp 1 Ngamdu, jihar Yobe, ranar Litinin, Attahiru ya ce manufarsa itace dakile ta'addanci kuma yana kyautata zaton kawo karshen yaki da Boko Haram, TheCable ta ruwaito.

"Zamu kara kaimi kan nasarorin da rundunar Operation Tura Takaibango suke samu domin kawo karshen wannan yaki," Attahiru yace.

"Wannan yakin zai zo karshe nan ba da dadewa ba. Za kuyi hakan tare da hadin kai da Sojojin Kamaru. Zamu dauko yan kasar Chadi domin tumurmushe yan ta'addan Arewa maso gabas."

DUBA NAN: Fulani Makiyayan dake kudancin Najeriya sun fara komawa jihar Kano, Miyetti Allah

Za mu dauko Sojin haya daga Chadi da Kamaru don kawar da yan Boko Haram, COAS
Za mu dauko Sojin haya daga Chadi da Kamaru don kawar da yan Boko Haram, COAS Credit: HQ NIgerian Army
Asali: Twitter

DUBA NAN: Shirin ciyar da yara 'yan makaranta ya samar da ayyuka 14,000 a Neja, Jami'i

Shugaban Sojin ya bayyana cewa yana sane da irin kalubalen da dakaru ke fama da shi kuma duk za'a magance su.

"Na samu labari daga wajen kwamandojinku kan rashin isassun kayan yaki. Ina da labarin rashin tufafin Soji da takalma. Muna kokarin sama muku takalma, da kayan kare kai cikin makonni masu zuwa," yace.

"Ina sane da matsalan dadewa a faggen fama babu sauyin waje. Ba zamu canza abin da gaggawa ba, amma ina tabbatar muku nan da wasu watanni zamu samar da wani tsarin kama-kama ta yadda wasu Soji zamu karba yakin daga hannunku. Ina ganin karshen wannan yaki kusa-kusa."

Attahiru ya bukaci dakarun su kara kaimi wajen yaki da yan ta'adda.

Kun ji cewa gabanin tabbatarwarsa da majalisar kasa, sabon shugaban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya ziyarci wasu rundunonin sojoji a jihar Borno.

Shugaban sojojin, wanda ya iso da safiyar ranar Litinin, ya samu rakiyar jami’ai daga OPL Lafiya Dole da runduna ta 7 zuwa hedikwatar rundunar kafin ya ci gaba da zuwa wasu wuraren.

Janar Attahiru, wanda ya karbi aiki daga hannun Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai makonni biyu da suka gabata, ya sake dawowa Maiduguri kwana bakwai bayan ziyarar da ya gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel