FG zata samar da wasu sabbin makarantu na musaman don koyar da ilimi a zamanance

FG zata samar da wasu sabbin makarantu na musaman don koyar da ilimi a zamanance

- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kammala shirin samar da wasu sabbin makarantu na zamani

- Dakta Hamid Bobboyi, babban sakataren hukumar ilimin bai daya (UBEC), shine ya sanar da hakan a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa

- A sanarwar da Mista David Apej na sashen yada labarai a UBE ya fitar, ya bayyana cewa tuni an fara gina hedikwatar makarantun a Abuja

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta kammala shirye shiryen gina makarantu na musamman don koyar da ilimi a zamanance a fadin kasar.

Babban sakataren hukumar ilimin bai ɗaya ta kasa (UBEC), Dr Hamid Bobboyi ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da wasu ayyuka da hukumar ilimin bai ɗaya ta gudanar a cikin jami'ar tarayya ta Dutse, da ke jihar Jigawa.

A cikin wata sanarwar dauke da sa hannun shugaban sashen watsa labarai na hukumar, Mr David Apej, babban sakataren ya kara da cewa ana kan gina wata babbar cibiyar nazarin ilimi na zamani a Abuja, wacce za ta kula da dukkanin ilimin bai ɗaya a fadin kasar.

KARANTA: Fahimta Fuska: Ganduje ya shirya muhawara tsakanin Abduljabar da manyan Malaman Kano

Idan aka kammala ginin cibiyar, ya jaddada cewa cibiyoyin za su taimaka wajen sanya ilimin bai ɗaya na kasar a cikin taswirar ilimin zamani na duniya, kamar yadda ThisDay ta rawaito.

A cewar Bobboyi, "Ilimin bai ɗaya kamar yadda kuka sani shi ne ginshiki na kowanne ilimi. Idan har aka samu nakasu daga wannan mataki na farko, to dukkanin bangarori na ilimi ya samu matsala."

FG zata samar da wasu sabbin makarantu na musaman don koyar da ilimi a zamanance
FG zata samar da wasu sabbin makarantu na musaman don koyar da ilimi a zamanance
Asali: UGC

Ya bayyana cewa hukumar UBEC a cikin shekaru hudu ta yi iya bakin kokarin ta wajen aiki tare da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi domin canja salon ba da ilimin bai ɗaya a kasar.

KARANTA: Duban kurilla: 'Yan Nigeria sun hango kurakurai biyu a jikin sabon katin APC na Tinubu

Tun farko a nata jawabin, shugabar jami'ar tarayya ta Dutse, Farfesa Fatima Butulu Mukhtar, ta godewa babban sakataren hukumar UBEC da kafatanin ma'aikatanta, bisa gina makarantar firamare da kuma cibiyar bayar da ilimin wuri (ECCDE) a cikin jami'ar.

A kwanakin baya ne Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta sanar da bullo da sabon shirin ASP (Alternate School Programme)

ASP sabon shirin gwamnatin Buhari ne da zai tabbatar da bayar da ilimi kyauta ga yara marasa galihu da basa zuwa makaranta.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa burin gwamnatinsa shine bayar da ilimi ga dukkan yaran da ke Nigeria.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel