Duban kurilla: 'Yan Nigeria sun hango kurakurai biyu a jikin sabon katin APC na Tinubu

Duban kurilla: 'Yan Nigeria sun hango kurakurai biyu a jikin sabon katin APC na Tinubu

- A ranar Asabar ne jagoran APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas ya sabunta shaidarsa ta zama mamba a jam'iyyar

- Jim kadan bayan ya kammala sabunta rijistarsa, Tinubu ya dauki hotuna tare da watsa su a kafafen sada zumunta

- Sai dai, da idanuwansu irin na mikiya, 'yan Nigeria sun hango wasu kura-kurai har guda biyu a jikin katin shaidar

Jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, a ranar Asabar, 6 ga watan Fabreru ya ziyarci cibiyar yin rejistar jam'iyyar da sabuntawa.

Bayan kammala ta shi rijistar, jagoran APC ya dauki hotuna tare da mutanen da ke wajen, wadanda daga bisani aka yada su a kafofin sada zumunta.

Wasu daga cikin yan Nigeria sun bata lokaci wajen binciken kwakwaf kan waɗannan hotunan, ko sun gano me su ke son ganowa? Tabbas sun gano.

KARANTA: Mamaki: APGA ta kayar da manyan jam'iyyu a zaben maye gurbin wakilin mazabar Magama/Rijau

Tinubu ya sabunta rijistar sa a ranar Asabar, 6 ga watan Fabreru, amma an sanya ranar 09/02/21 a matsayin ranar da Tinubu ya yi rejista.

Duban kurilla: 'Yan Nigeria sun hango kurakurai biyu a jikin sabon katin APC na Tinubu
Duban kurilla: 'Yan Nigeria sun hango kurakurai biyu a jikin sabon katin APC na Tinubu
Source: Twitter

Da idanuwansu kamar na Mikiya, wasu yan Nigeria sun gano kuskure na biyu; 29 ga watan Maris ne jagaban jam'iyyar ya yi bukin zagayowar ranar haihuwar sa, amma an cika fom din ne a ranar 27 ga watan Maris, 1952.

KARANTA: An kama matasan da ke dillancin hotuna da bidiyon tsiraicin 'yammatan Kano a yanar gizo

Wasu daga cikin 'yan Nigeria da suka mayar da martani akan kurakuran da ke jikin katin sun yi barkwanci ta hanyar tambayar Tinubu ya basu sirri da bayanai akan irin kalendar da yake amfani da ita domin suma ranakun rayuwarsu s kasance a gaba da na sauran mutane.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa Cif John Odigie-Oyegun, tsohon shugaban jam'iyyar APC, ya ki amincewa da ra'ayin Tinubu da Akande akan sabunta rijista.

Dattijo a APC, Bisi Akande, ya soki aikin sabunta rijistar mambobin jam'iyyar da shugabanci riko a karkashin Mai Mala Buni ke cigaba da gudanarwa.

A yayin da ya ke karbar sabuwar rijitarsa a ranar Asabar, Tinubu ya bayyana cewa yana goyon bayan ra'ayin Akande akan cewa babu bukatar aikin sake sabunta rijistar mambobi.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel