Gwamna Zulum ya rabawa Mata 16, 000 miliyoyin kudi da abinci, zai gina gidajen Malamai

Gwamna Zulum ya rabawa Mata 16, 000 miliyoyin kudi da abinci, zai gina gidajen Malamai

- A 2014 ne Boko Haram su ka rugurguza gidajen Malamai a Gwoza

- Gwamnatin Borno za ta sake gina wadannan gidaje 33 da aka rusa

- Babagana Zulum ya taimakawa mata har 16, 000 da kudi da abinci

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince ya sake gina gidaje 33 da aka rusa a rukunin gidajen malamai a garin Gwoza.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa mai girma gwamnan ya bada umarni a gina wadannan gidaje ne bayan ya gana da malaman da ke Gwoza.

Mai magana da yawun bankin gwamnan, Malam Isa Gusau, ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar.

Malam Isa Gusau ya ce a 2014 ne ‘yan ta’addan kunggiyar Boko Haram su ka kona wadannan gidaje da malaman makarantun boko su ke zama.

KU KARANTA: Gawurtattun ‘Yan bindigan Jihar Zamfara za su ajiye makamai

Bayan haka, gwamnatin Babagana Umara Zulum ta bada umarnin daukar sababbin malaman makaranta shida da za su yi aiki a karamar hukumar Gwoza.

Har ila yau, gwamna Babagana Umara Zulum ya raba kayan abinci ga wasu mata 16, 000 da su ke sansanin gudun hijira, bayan dawowarsu gida a ranar Lahadi.

Malam Isa Gusau ya ce Gwamnan ya kuma ba duka wadannan mata gudumuwar kudi N5, 000.

Wannan rabon kudi har Naira miliyan 80 ya na cikin yunkurin da Zulum ya ke yi na ganin an rage radadin da mutane su ka shiga a dalilin rikicin Boko Haram.

Zulum ya yi wa Malamai sha-tara ta arziki, ya haramta dabar siyasa a Borno
Gwamna Babagana Zulum Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

KU KARANTA: Sai Jam’iyyarmu ta APC ta shafe shekara 100 ta na mulki – Hon. Gagdi

A karshen makon ne dai gwamnan ya bada sanarwar haramta duk wani nau’i na bangar siyasa. Gwamnati za ta dauki mataki a kan wanda aka kama da laifi.

Dazu kun ji Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce rashin hadin kai tsakanin gwamnonin yankin Arewa ya sa aka gagara samun zaman lafiya.

Da aka yi hira da shi a BBC Hausa, gwamna Nasir El-Rufai ya soki yunkurin zaman sulhun da wasu malamai da shugabanni su ke yi da masu addabar al'umma.

Gwamnan ya ce duk 'dan bindigan da ya saba karbar miliyoyi ta muguwar hanya, ba zai tuba ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel