Gwamnan jihar Rivers ya kai ziyara Sokoto kan gobarar kasuwa, ya bada gudunmuwar N500m

Gwamnan jihar Rivers ya kai ziyara Sokoto kan gobarar kasuwa, ya bada gudunmuwar N500m

- Nyesom Wike ne gwamna na farko da kai wa jihar Sokoto ziyara tun bayan gobaran kasuwa

- Akwai kyakkyawan alaka tsakanin Tambuwal da Wike, dukkansu yan jam'iyyar PDP

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya kai ziyara jihar Sokoto don jajantawa takwararsa, gwamna Aminu Waziri Tambuwal, bisa mummunar gobarar kasuwar da ta faru ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.

A ziyarar, Wike ya baiwa gwamnatin jihar gudunmuwar milyan dari biyar domin sake gina kasuwar.

Hakazalika ya kai ziyara fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubuakar Sa'ad.

Gwamnan jihar Rivers ya kai ziyara Sokoto kan gobarar kasuwa, ya bada gudunmuwar N500m
Gwamnan jihar Rivers ya kai ziyara Sokoto kan gobarar kasuwa, ya bada gudunmuwar N500m Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Saura kiris mu cire 'yan Najeriya 20m daga kangin talauci - Osinbajo

Gwamnan jihar Rivers ya kai ziyara Sokoto kan gobarar kasuwa, ya bada gudunmuwar N500m
Gwamnan jihar Rivers ya kai ziyara Sokoto kan gobarar kasuwa, ya bada gudunmuwar N500m Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

KU DUBA: Ooni da Ataoja sun ba takarar tsohon Gwaman Legas, Bola Tinubu goyon-baya

Jiya mun kawo muku cewa gobara ta tashi a wani bangare na babbar kasuwar Sokoto misalin karfe 5 na asubahi na ranar Talata 19 ga watan Janairun 2020, TVC ta ruwaito.

Bidiyon gobarar ya nuna ma'aikatan kwana kwana, yan sanda da jami'an hukumar kiyayye haddura ta kasa, FRSC da wasu yan kasuwa na kokarin kashe gobarar.

Kawo yanzu ba a san anihin abinda ya yi sanadin afkuwar gobarar ba.

Kamar yadda ya ke a cikin bidiyon, dandazon al'umma sun taru wasu sun hau kan motocci suna kallon yadda ake kokarin kashe wutar.

Mahukunta su kan janyo hankulan mutane a kan yin takatsantsan da wuta musamman a irin wannan yanayi na bazara da iska ke kadawa sosai kuma mutane ke amfani da wuta don jin dumi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel