Abuja: 'Yan bindiga sun shiga har gida sun yi awon gaba da tsohon ACG NIS, Ibrahim Idris, da iyalinsa
- Masu garkuwa da mutane cikin kakin soji sun ci karensu babu babbaka a garin Tungan Maje da ke Gwagwalada a Abuja
- Shaidar gani da ido ya bayyana cewa 'yan bindigar sun shafe akalla awanni uku suna cin karensu babbaka a garin
- Daga cikin mutane hudu da 'yan bindigar suka yi awon gaba da sub akwai tsohon mataimakin shugaban hukumar NIS
Masu garkuwa da mutane sun sace wasu mutane hudu a wani hari da suka kai garin Tungan Maje da ke karamar hukumar Gwagwalada.
Wani shaidar gani da ido ya sanar da Jaridar TheCable cewa masu garkuwa da mutane sun shafe kusan awanni uku; daga 12:00 na dare zuwa karfe 3:00 na safiyar Lahadi, suna cin karensu babu babbaka kafin daga bisani su yi awon gaba da mutanen.
Daga cikin mutanen da aka sace akwai Abdullahi Idris Rakieu, tsohon mataikin shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS), tare da wasu mutane biyu daga cikin iyalansa.
KARANTA: Rijista: An tashi baran-baran ba shiri bayan rikici ya barke yayin taron shugabannin APC
Kazalika, 'yan ta'ddar, wadanda ke sanye cikin kakin soji, sun yi awon gaba da wani mutum mai suna Olusola Agun.
KARANTA: An kama matasan da ke dillancin hotuna da bidiyon tsiraicin 'yammatan Kano a yanar gizo
'Yan bindigar sun shiga gidaje da dama a garin ta hanyar balle kofa da kuma karya tagogin dakuna bayan sun tsallaka gidan mutane.
A kwanakin baya ne Legit.ng ta rawaito cewa jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kano sun kai samame tare da cafke wasu mutane hudu da ake zargi da garkuwa da mutane.
Daga cikin mutanen hudu da suka shiga hannu har da wata mace da rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa an kashe mijinta a cikin 'yan bindiga a jihar Zamfara.
Matar ta shiga sana'ar garkuwa da mutane bayan an kashe mijinta, wanda shi ma dan ta'adda ne, a cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng