Hukuma ta hukunta Emerson Carioca a dalilin tube wando da ya zura kwallo a raga

Hukuma ta hukunta Emerson Carioca a dalilin tube wando da ya zura kwallo a raga

- Emerson Carioca ya cire wando saboda murnar jefa kwallo a wasa a fili

- Hukuma ta dauki mataki, ta hukunta wannan ‘dan wasa mai shekara 25

- Carioca ya ce yayi hakan ne saboda ‘yan wasan Marica su na ta zagin shi

An lafta wa ‘Dan wasan kasar Brazil, Emerson Carioca hukuncin yin wasanni takwas ba tare da ya buga ba saboda laifin da ya yi a karshen 2020.

Jaridar The Sun ta ce Emerson Carioca ya fito da tsaraicinsa a fili bayan ya ci kwallo a Disamban shekarar da ta gabata, wannan ya sa aka hukunta shi.

‘Dan kwallon mai shekara 35 ya tube bangaren wandonsa, inda ya kusa yin zindir saboda murnar ya jefa kwallo a wasan Sampaio Correa da Marica.

Wannan kwallo da Emerson Carioca ya ci, ya yi sanadiyyar da kungiyarsa a lokacin ta samu damar zuwa gasar cin kofin the Carioca Championship.

KU KARANTA: Koci da Shugaban Real Madrid sun kamu da COVID-19

Hotuna sun tabbatar da cewa, da Carioca ya zura kwallo a raga, ya zo wajen abokan karawarsa, ya tube wando, ya rika karkada al’aurarsa da nufin fusata su.

‘Dan wasan gaban ya yi nasarar harzuka ‘yan wasan kungiyar Marica, har rigima ta kaure a filin kwallo.

Duk da Carioca ya bar kungiyar Sampaio Correa bayan wannan abu ya faru, ya koma wata kungiya a kasar Portugal, hukuncin da aka yi masa ya bi shi.

Globo Esporte ta ce kungiyar da ‘dan wasan ya koma sun daukaka kara domin ayi watsi da wannan hukunci da aka dauka a kan ‘dan wasan da ya yi nadama.

Hukuma ta hukunta Emerson Carioca a dalilin tube wando da ya zura kwallo a raga
Emerson Carioca Hoto: Shafin Emersoncariocaoficial
Asali: UGC

KU KARANTA: Ahmed Musa zai koma Wes Brom

An samu Carioca da laifin saba doka, shiga rigima, da jawo fada a cikin wasa. Amma ya ce ya yi hakan ne domin martani ga ‘yan wasan Marica da ke gulmarsa.

A Najeriya, kun ji Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya bayyana ainihin abin da ya jawo har ta’adin ‘yan bindiga ya yi kamari sosai a yankin Arewa maso yamm.

Malamin ya yi magana bayan ya hadu da ‘Yan bindiga a Zamfara, ya ce ta’addanci ne ba tsageranci ba.

Ahmad Gumi ya bayyana cewa rashin kula ne ya jawo wadannan mutane su ka zama gawurtattun ‘yan ta’adda, ya bada shawara ayi sulhu da su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel