Allah ya yi wa kawun Sheikh Isa Ali Pantami rasuwa

Allah ya yi wa kawun Sheikh Isa Ali Pantami rasuwa

- Ministan sadarwar da tattalin arzikin zamani na Nigeria, Sheikh Dr Isa Ali Pantami ya yi babban rashi

- A daren ranar Laraba 3 ga watan Fabrairu ne ministan ya sanar da cewa kawunsa, Alhaji Isa Ibrahim ya rasu a Gombe

- Al'umma da dama sun garzaya shafin Twitter na ministan domin yi masa ta'azziya da addu'a ga mamacin

Alhaji Isa Ibrahim, kawun ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Nigeria, Sheikh Dr. Isa Ali Pantami ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne a ranar Laraba 3 ga watan Fabrairun shekarar 2021 a garin Gombe bayan gajeruwar rashin lafiya kamar yadda ministan ya sanar a shafinsa na Twitter.

Allah ya yi wa kawun Sheikh Pantami rasuwa
Allah ya yi wa kawun Sheikh Pantami rasuwa. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa Farfesa Dahiru Yahaya rasuwa a Kano

Ya yi addua'ar Allah ya jikansa da rahama ya gafarta masa kurakurensa da ma sauran iyaye da yan uwa da suka rasu.

Ministan ya kara da cewa tabbas mutuwar kawunsa ya masa ciwo matuka.

Yan Nigeria da dama sun yi tururuwa zuwa shafin ministan domin yi masa ta'aziyyar rasuwar kawunsa.

Cikinsu akwai Bashir Ahmad mai taimakawa shugaba Muhammadu Buhari a bangaren sabbin kafafen watsa labarai.

Inda shima ya yi addu'ar Allah ya jikan marigayin ya kuma saka masa da gidan aljannah.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel