'Mu ma abin ya ishe mu', 'Yan Bayelsa sun nemi a fattaki makiyaya daga jiharsu

'Mu ma abin ya ishe mu', 'Yan Bayelsa sun nemi a fattaki makiyaya daga jiharsu

- Mata a jihar Bayelsa sun yi zanga-zangar neman gwamnati ta dauki mataki kan makiyaya a jihar

- Matan sun fito sun rufe wasu titunan garin inda suke cewa sun gaji da makiyayan da shanunsu

- Wasu daga cikinsu sunyi ikirarin cewa duk da cewa gwamnatin ta ware wa makiyayar wurinsu su kan shiga gonaki

Mata daga garuruwan Epie da Atissa a karamar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa sun yi zanga zanga a ranar Laraba kan abinda suka kira fitinar makiyaya a garuruwansu.

Yayin da suke rike da ganye a shataletalen Etegwe-Edepie a Yenagoa, matan sun rika rere wakokin hadin kai cikin harshensu, The Cable ta ruwaito.

'Mu ma abin ya ishe mu', 'Yan Bayelsa sun nemi a fattaki makiyaya daga jiharsu
'Mu ma abin ya ishe mu', 'Yan Bayelsa sun nemi a fattaki makiyaya daga jiharsu. Hoto: @thecableng
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano ta hana Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wa'azi a jihar

Sun kuma rufe wasu manyan tituna wanda hakan ya janyo cinkoso a titunan.

Matan sun koka cewa makiyaya sun kyalle shanunsu sun lalata musu kayan abinci a gonakinsu.

Daya daga cikin masu zanga-zangar da ta ce sunan ta Mercy Adovuya, ta ce ba su bukatar shanu a garinsu don haka gwamnati ta dauki mataki a kan lamarin.

"Ba zai yiwu mu cigaba da rufe bakunan mu ba a kan wannan matsalar. Ba mu son shanu a garin mu. Lokaci ya yi da gwamnati za ta dauki mataki kafin wani abu ya faru.

"Abin ya isa haka. Makiyaya su bar gonakin mu. Gwamnatin jiha ta kare mu da gonakin mu daga makiyaya da shanunsu."

KU KARANTA: Allah ya yi wa kawun Sheikh Isa Ali Pantami rasuwa

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson yayin mulkinsa ya ware wani gonan kwakwa na gwamnati domin makiyaya su rika kiwo a garin Elebele don hana su kiwo barkatai a babban birnin jihar.

An saka alamar hana kiwo a wasu wurare amma duk da haka wasu makiyayan na shiga gonakin manoma.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel