Tofa: Idan yan arewa suka fara rama abinda ake yi wa yan uwansu a kudu abin ba zai yi kyau ba

Tofa: Idan yan arewa suka fara rama abinda ake yi wa yan uwansu a kudu abin ba zai yi kyau ba

- Alhaji Bashir Tofa ya gargadi gwamnatin tarayya ta dauki mataki kan yan kudu da ke tsangwamar makiyaya fulani a yankinsu

- Dattijon na arewa ya ce wasu makiya Nigeria ne ke amfani da wannan damar domin neman tada zaune tsaye

- Ya ce idan mutanen yankin arewa suka fara yin ramuwar gayya kan abinda yan kudu ke yi wa yan uwansu zai yi wahala a magance lamarin

Dattijon Arewa, Bashir Tofa, ya yi gargadin cewa wadanda ke neman tada rikicin kabilanci a kasar su dena domin kare afkuwar babban tashin hankali.

Ana zaman dar dar ne a kasar tun bayan da aka bawa makiyaya wa'adin kwanaki su fice daga yankin kudu maso yamma kan karuwar hare hare da rashin tsaro.

Sunday Igboho, wani mai kare hakkin Yarbawa ya fara tada rikicin a watan Janairu a jihar Oyo wadda ya janyo rasa rayyuka da dukiyoyi.

Tofa: Idan yan arewa suka fara rama abinda ake yi wa yan uwansu a kudu abin ba zai yi kyau ba
Tofa: Idan yan arewa suka fara rama abinda ake yi wa yan uwansu a kudu abin ba zai yi kyau ba. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau kan almundahar kwangilar N260m

Sai dai an samu zaman lafiya bayan da wasu masu ruwa da tsaki daga yankin kudu da arewa suka gana a karamar hukumar Ibarapa da ke jihar Oyo a lokacin da rikicin ya fara.

Sai dai abin mamaki Igboho ya kuma tafi jihar Ogun don cigaba da abinda ya fara a Oyo inda rahotanni suka ce an kashe mutum daya bayan rikici ya barke.

A sanarwar da ya fitar, Tofa, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki mataki a kan lamarin kafin ya kazanta, Daily Trust ta ruwaito.

"Ba zamu amince da kashe kashen al'umma musamman Fulani da ake yi ba a wasu sassan kasar. Wasu makiya Nigeria ne ke neman tarwatsa kasar.

DUBA NAN: NANS ta gargadi Igboho: Kada ka janyo fitina a Kudu maso yamma

"Mutane na fusata, idan aka fara ramuwar gayya a kan yan kudu a nan arewa, zai yi wahala a magance lamarin. Makiyar mu na gida da waje wadanda hukumomin tsaro sun san su na kokarin hada mu fada domin ganin mun kai matsayin da ba za a iya gyara ba.

Babu yankin kasar nan da ke zaune lafiya.

Tofa ya yi kira ga shugaban kasa ya dauki mataki a kan lamarin kafin abubuwa su tabarbare.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164