Basaraken Ondo ya rasu bayan shafe shekaru 43 kan karagar mulki

Basaraken Ondo ya rasu bayan shafe shekaru 43 kan karagar mulki

- Allah ya yi wa basaraken garin Isikan a jihar Ondo, Oba Joseph Olu-Ojo rasuwa

- Oba Joseph Olu-Ojo ya rasu bayan shafe shekaru 43 a kan karagar mulki

- Kafin nadinsa a shekarar 1978, , Oba Joseph Olu-Ojo ya yi aiki a babban asibitin Akure na jihar Ondo

Basaraken garin Isikan a karamar hukumar Akure ta Kudu a jihar Ondo, Oba Joseph Olu-Ojo ya riga mu gidan gaskiya bayan shafe shekaru 43 a kan karagar mulki.

Daya daga cikin yayan basaraken, Yarima Dapo Ojo, ya tabbatar da rasuwarsa a ranar Laraba, The Punch ta ruwaito.

Basaraken Ondo ya rasu bayan shafe shekaru 42 kan karagar mulki
Basaraken Ondo ya rasu bayan shafe shekaru 42 kan karagar mulki. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: FG ta fara sayar da gwala-gwalen Diezani, gidajen Badeh da wasu kayayyakin da ta kwace

Ya ce, "Baba ya tafi. Ta faru yau. Mun gode wa Allah bisa rayuwar da ya yi."

An gano cewa Oba Olu-Ojo ya hau karagar mulki ne a ranar 3 ga watan Yulin 1978, a matsayin Iralepo na Isikan na 37 bayan rasuwar magabacinsa, Oba Aladeyoyinbo a shekarar 1976.

Marigayin sarkin ya samu horaswa a matsayin kwararren mai bada magani a babban asibitin Akure, kuma yana daya daga cikin ma'aikatan da suka fara aiki a asibitin da aka kafa a 1953.

Baya ga aiki a dakin bada maganin, marigayi sarkin ya cigaba da aiki har ya kai matsayin mai kula da dakin ajiye kayayyaki a asibitin bayan ya samu horasawa daga makarantar horas da masu tsaron dakin ajiyar kaya a Legas.

KU KARANTA: Jerin abubuwa hudu da aka haramtawa makiyaya aikatawa a Ekiti

Oba Olu-Ojo ya yi murabus daga aikin asibiti a shekarar 1978 a lokacin da aka nada shi sarkin Isikan kuma ya shafe shekaru 43 a kan mulki.

Shine sarki da ya fi dadewa kan mulki a tarihin Iralepos.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel