DMGS: Kyawawan hotunan makarantar sakandare na Najeriya mai shekaru 96

DMGS: Kyawawan hotunan makarantar sakandare na Najeriya mai shekaru 96

- Dennis Memorial Grammar School (DMGS), wacce aka kafa a 1925, ta kasance daya daga cikin makarantu mafi tsufa a Najeriya

- Makarantar wacce ta cika shekaru 96 kwanan nan ta samar da farfesoshi da dama da wasu manyan mutane a kasar

- Daga cikinsu, DMGS ta samar da farfesan tarihi na farko a Najeriya, Farfesa Kenneth Onwuka Dike

Makarantar Dennis Memorial Grammar School (DMGS), wacce ta kasance makarantar sakandare na farko-farko a Onitsha, jihar Anambra, ta cika shekaru 96 da kafuwa.

An kafa makarantar a ranar 25 ga watan Janairun 1925.

A bisa ga wata wallafa a shafin Facebook na The Nigerian Nostalgia 1960-1980 Project, wanda ya tattara hotunan makarantar, DMGS ta samar da farfesoshi da dama a Najeriya.

DMGS: Kyawawan hotunan makarantar sakandare na Najeriya mai shekaru 96
DMGS: Kyawawan hotunan makarantar sakandare na Najeriya mai shekaru 96 Hoto: Uchechukwu Christopher Muoneke via The Nigerian Nostalgia 1960 -1980 Project
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Korona: Ku yi allurar rigakafi ko ku mutu, FG ta gargadi yan Nigeria

An tattaro cewa makarantar ta samar da farfesan tarihi na farko a Najeriya, Farfesa Kenneth Onwuka Dike wanda aka ce ya riki mukamin shugabn dalibai na DMGS a 1936.

DMGS ta kuma samar da farfesan lissafi na farko a Najeriya, Farfesa James O. C. Ezeilo (ya kammala makarantar a shekarar 1948), farfesan Pharmacology na farko a Najeriya, Farfesa Gilbert O. Onuaguluchi (ya kammala makarantar a shekarar 1944).

Sai Mr Samuel Onochie Ogoaz i(ya kammala makarantar a shekarar 1939), Farfesa Kenneth Onwuka Dike (ya kammala makarantar a shekarar 1936).

An kuma tattaro cewa makarantar mai dimbin tarihi ta samar da likitan soji na farko a Najeriya, HRH Igwe. Captain Sir. Dr. Walter C. Eze (ya kammala makarantar a shekarar 1945), masanin ilimin duwatsu na farko a Naeriya, Prince Alexander Okoli (ya kammala makarantar a shekarar 1953).

Injiniyan man fetura na farko a Najeriya, Engr. Dr Emmanuel Egbogah (ya kammala makarantar a shekarar 1961), Dan kabilar Igbo na farko da ya zama injiniya, , Engr. Isaac Iweka (ya kammala makarantar a shekarar 1930), da sauransu.

DMGS: Kyawawan hotunan makarantar sakandare na Najeriya mai shekaru 96
DMGS: Kyawawan hotunan makarantar sakandare na Najeriya mai shekaru 96 Hoto: @ConnectOnitsha
Asali: Twitter

A wani labarin, majalisar zartarwa ta tarayya, FEC, a ranar Laraba, ta amince da kafa karin jami’o’i 20 masu zaman kansu a kasar.

KU KARANTA KUMA: Tsohuwar da bata samu haihuwa ba ta ce ita da kanta ta nema wa mijinta sabuwar mata

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa amincewar ta biyo bayan wani rubutu da Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya gabatar yayin taron yau wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Tara daga cikin jami’o’i masu zaman kansu suna Arewa maso Tsakiya, uku a Kudu maso Kudu, biyu a Kudu maso Gabas, biyar daga cikinsu a Arewa maso Yamma da kuma daya a Kudu maso Yamma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng