Kuma dai: Ma'aikatan Jami'o'i za su fara sabon yajin aiki a watan Fabrairu

Kuma dai: Ma'aikatan Jami'o'i za su fara sabon yajin aiki a watan Fabrairu

- Ma'aikatan jami'a SSANU da NASU za su tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani a watan gobe

- Sun bawa gwamnati wa'adin sati biyu don daukar mataki daga yau Juma'a zuwa 5 ga Fabarairu

- Sun ce wata uku bayan gwamnati ta yi musu alkawari har yanzu an gaza daukar mataki wanda shi ne dalilin yajin aikin

Kungiyar Manyan Ma'aikatan jami'o'i (SSANU) da na Ma'aikata Marasa Koyarwa (NASU) sun bayyana tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga 5 ga watan Fabarairu, Channels TV ta ruwaito.

Da ya ke bayyana matakin ranar Juma'a a Abuja, mai magana da yawun kwamitin hadin gwiwar SSANU da NASU, Peter Adeyemi, ya yi bayani cewa gwamnatin tarayya ta saba yarjejeniyar da suka cimma a watan Oktobar shekarar da ta gabata wanda hakan ya janyo daukar matakin.

Ma'aikatan jami'a za su fara jayin aiki a watan gobe
Ma'aikatan jami'a za su fara jayin aiki a watan gobe. Hoto: @Channelstv
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Jerin manyan kyaututuka masu tsada 10 da aka yi wa Donald Trump

Yajin aikin na bukatar a cire ma'aikatan su daga tsarin biyan albashi na (IPPIS) da kuma sake duba tsarin kasafin kudin alawus tsakanin su da malaman jami'a.

"Kwamitin hadin gwiwa na SSANU da NASU ya yanke shawara kamar haka:

Ma'aikatan NASU/SSANU su tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani daga ranar 5 ga Fabarairu, 2021," a cewar sa.

"Wa'adin sati biyu kenan daga yau, Juma'a, 22 ga Janairu 2021 ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki don daukar mataki.

KU KARANTA: Gwamnatin Jihar Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki

"Yarjejeniyar da muka sanya hannu akai cikin watan Oktoba ta ce za a duba bukatar mu cikin mako biyu.

"Amma bayan wata uku yanzu, ba a gyarq ko daya a cikin matsalolin ba, wanda ya jawo wa mambobin mu matsala wanda albashin su baya cika sanadiyar IPPIS."

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel