A yau Gwamnatin Tarayya za ta yi zama da Shugabannin SSANU da NASU

A yau Gwamnatin Tarayya za ta yi zama da Shugabannin SSANU da NASU

- Kungiyoyin SSANU da NASU za su zauna da Gwamnatin Tarayya yau

- Ministan kwadago ya tabbatar da cewa za ayi zama da ‘Yan kwadagon

- Ana sa rai a shawo kan ma’aikatan jami’an da ke neman yin yajin-aiki

Daily Trust ta ce wakilan gwamnatin tarayya da na bangaren kungiyoyin SSANU da NASU na ma’aikatan jami’a za su yi zama a ranar Talata.

Kungiyoyin na Senior Staff Association of Nigerian Universities (SSANU) da Non-Academic Staff Union (NASU) su na yunkurin tafiya yajin-aiki.

A yau 2 ga watan Fubrairu, 2021, ake sa ran gwamnatin tarayya za ta gana da wakilan kungiyoyin domin hana su shiga yajin-aikin da suke shiri.

Jaridar ta bayyana cewa Ministan kwadago da samar da aikin yi na kasa, Dr. Chris Ngige ne zai jagoranci bangaren gwamnatin tarayya a taron da za ayi.

KU KARANTA: SSANU, NASU sun yi zanga-zangar lumana a kan tsarin IPPIS

A gefe guda kuma, shugaban kungiyar SSANU na kasa baki daya, Malam Mohammed Ibrahim Haruna, shi ne wanda zai jagoranci kungiyoyin kwadagon.

An samu sabani ne tsakanin ma’aikatan jami’o’in a sakamakon alawus da gwamnatin tarayya ta fitar, kungiyoyin SSANU da NASU ke ganin an kware su.

Gwamnati ta fitar da kudi har Naira biliyan 40 da sunan alawus din karin aiki da ma’aikatan jami’a su kayi, amma kungiyar ASUU ce ta tashi da kaso mai tsoka.

Ministan kwadagon ya bada sanarwar zai yi zama da kungiyoyin kwadagon a yau ne ta bakin mai magana da yawun bakin ma’aikatarsa, Mista Charles Akpan.

KU KARANTA: Ma'aikatan Jami'o'i za su fara sabon yajin aiki a watan Fabrairu

A yau Gwamnatin Tarayya za ta yi zama da Shugabannin SSANU da NASU
Gwamnatin Tarayya da shugabannin SSANU da NASU Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Akpan ya ce makasudin zaman shi ne a samu ayi sulhu tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da bangaren hadaka na kungiyoyin SSANU da kuma NASU.

A baya kun ji cewa Ibrahim Haruna da sauran ‘yan kungiyarsu sun yi barazanar shiga yajin aiki a ranar 5 ga watan nan saboda yadda aka shirya za a raba kudin.

Sauran kukan da SSANU da NASU su ke yi shi ne matsalar da ake samu da manhajar IPPIS da aka kirkiro domin biyan albashin ma’aikatan gwamnati a kasar.

Haka zalika kungiyoyi na wadannan ma’aikata wadanda ba su koyar wa sun ce ana bata lokaci wajen sake tattauna yarjejeniyar 2009 da aka yi da gwamnati.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel