Shugaban Real Madrid Perez ya kamu da COVID-19

Shugaban Real Madrid Perez ya kamu da COVID-19

- Florentino Perez, shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ya kamu da korona

- Kungiyar ta sanar da hakan ne cikin wani sako da ta fitar a ranar Talata

- Sanarwar ta ce amma a halin yanzu baya nuna alamun cutar ta korona

Shugaban kungiyar kwallon kafa na Real Madrid Florentino Perez mai shekaru 73 ya kamu da cutar covid 19 kamar yadda kungiyar ta sanar a ranar Talata, The Punch ta ruwaito.

Kungiyar da ke rike da kofin kwararru na kasar Spain cikin sanarwar da ta fitar ta ce Perez "baya nuna wasu alamun cutar a halin yanzu."

Shugaban Real Madrid Perez ya kamu da COVID-19
Shugaban Real Madrid Perez ya kamu da COVID-19. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu yanzu: 'Yan PDP sun yi arangama da jami'an tsaro a Ebonyi

An gano cewa Perez na dauke da cutar ne bayan mai horas da yan wasar kungiyar ta Real Madrid, Zinedine Zidane shima ya kamu da cutar a makon da ta gabata.

Zidane shima baya nuna alamun cutar kuma ya dawo filin horas da yan wasa na Madrid a safiyar ranar Talata bayan ya kebe kansa na wasu kwanaki.

Perez yana wa'adinsa na biyu a matsayin shugaban kungiyar Real Madrid wacce ta fara daga shekarar 2009. Shine kuma ya kula da kungiyar daga 2000 zuwa 2006.

KU KARANTA: EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau kan almundahar kwangilar N260m

Sanarwar ta ce: "Real Madrid ta tabbatar da cewa shugaban mu Florentino Perez ya kamu da kwayar cutar COVID19 dama an saba yi masa gwajin lokaci zuwa lokaci, duk da cewa baya nuna wasu alamu."

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel