Da duminsa: Malamin makaranta ya aike da 'yan sanda 3 lahira

Da duminsa: Malamin makaranta ya aike da 'yan sanda 3 lahira

- Wata kotu a jihar Benuwe ta bukaci a adana mata wani malamin makaranta a gidan gyaran hali

- Ana zarginsa da kashe 'yan sanda uku bayan kutsawa gidan shugaban karamar hukumar Katsina-Ala

- Wanda ake zargin mai suna Mernyi Christopher ya amsa laifinsa inda yace ba shi kadai bane ya aikata

Wata kotun majistare dake Makurdi a ranar Talata ta bada umarnin adana wani malamin makaranta mai suna Mernyi Christopher a gidan gyaran hali sakamakon halaka 'yan sanda uku da yayi.

'Yan sandan sun zargi malamin da laifuka da suka hada kai wurin aikata laifi, fashi da makami, ta'addanci da kuma kisan kai, Vanguard ta wallafa.

Alkalin kotun, Ajuma Igama wanda bai saurari rokon Christopher ba, ya ba 'yan sanda umarnin mika takardun shari'ar ofishin daraktan hukunci.

KU KARANTA: Hotunan karen wata 6 da za a siyar N1.1m ya janyo cece-kuce a kafar sada zumunta

Da duminsa: Malamin makaranta ya aike da 'yan sanda 3 lahira
Da duminsa: Malamin makaranta ya aike da 'yan sanda 3 lahira. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Igama ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 25 ga watan Fabrairun 2021 domin cigaba da shari'ar.

Tun farko, dan sanda mai gabatar da kara Sajan Ato Godwin ya sanar da kotun cewa rundunar Operation Zanda ta damke Christopher a cikin kungiyar tantiran da ke addabar garin Katsina -Ala.

An zargi kungiyar da kutsawa gidan Alfred Avalumun, shugaban karamar hukumar Katsina-Ala a ranar 24 ga watan Disamban 2020 kuma suka kashe 'yan sanda uku tare da yin awon gaba da bindigogi.

A yayin binciken hukumar 'yan sanda, wanda ake zargin ya amsa laifinsa tare da wani Aondofa Chekele da wasu wadanda har yanzu ba a kama su ba.

Dan sanda ya ce har yanzu ana cigaba da bincike kuma ya roki kotun da ta dage sauraron shari'ar.

KU KARANTA: Hotunan saukar Sunday Igboho jihar Ogun domin fatattakar Fulani makiyaya

A wani labari na daban, Anthony Ezonfade Okorodas wani alkali ne a jihar Delta wanda ya bada labarin yadda gwajin DNA ya bankado cewa ba shi ne mahaifin 'ya'yansa uku ba da tsohuwar matarsa.

A wata takarda da ya bai wa manema labarai a ranar 28 ga watan Janairu, Okorodas ya ce ya yanke hukuncin fallasa sirrin ne domin gujewa maganganun jama'a da kuma karya da za a yi a kansa.

Alkalin ya zargi Celia Juliet Ototo, tsohuwar matarsa da barin aurensu na shekaru 11 a lokacin da autansu yake da shekaru shida a duniya, The Cable ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: