Hotunan karen wata 6 da za a siyar N1.1m ya janyo cece-kuce a kafar sada zumunta

Hotunan karen wata 6 da za a siyar N1.1m ya janyo cece-kuce a kafar sada zumunta

- Wani dan Najeriya ya wallafa hotunan karensa mai watanni 6 da haihuwa da yake so ya siyar N1,100,000

- Mutane da dama sun yi ta caccakarsa akan tsadar karen har suna tambaya idan zai iya zama fasfotin Canada

- Hotunan tsadadden karen sun yi ta yawo a kafafen sada zumunta inda mutane suka yi ta tsokaci iri-iri akai

Wani mutum mai amfani da suna KidMarleymusic a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ya janyo cece-kuce bayan ya wallafa hotunan karensa da yake son siyarwa N1,100,000.

A cewarsa karen ya cika watanni 6 da haihuwa. Mutane sun yi ta mamaki akan tsabar tsadar karen, har suna tambaya idan wannan kare yana da wani muhimmanci ne na daban akan sauran karnuka.

Hotunan karen wata 6 da za a siya N1.1m ya janyo cece-kuce a kafar sada zumunta
Hotunan karen wata 6 da za a siya N1.1m ya janyo cece-kuce a kafar sada zumunta. Hoto daga @Kidmarleymusic
Source: Twitter

KU KARANTA: Dalilin da yasa Buratai da sauran tsoffin hafsoshin tsaro suka gaza, Wike ya fasa kwai

Akwai wadanda har zolayarsa suka yi, cikin wasa suna tambayarsa idan gida zai sayar, ko kare ko kuma duka saboda basu ga dalilin da zai sa dabba yayi wannan tsadar ba.

Wadanda kuma suka fahimci kyau da muhimmancin karen har tambayarsa wurin da yake da zasu je su duba karen su yi ciniki suka yi.

KU KARANTA: Hotunan ganawar Zulum ta farko da sabbin hafsoshin tsaro, ya mika manyan bukatu 3

A wani labari na daban, jama'a da suka halarci sallar Juma'a a ranar 29 ga watan Janairun 2021 a masallacin Al Noor da ke Abuja sun sha matukar mamaki.

Lamarin mai cike da ban mamaki ya auku ne bayan da aka daura auren wata amarya kuma aka damka kudin sadakinta N100,000 ga waliyyinta amma suka yi batan dabo.

Tuni kuwa waliyyin amaryar ya bayyana batan kudin, lamarin da yasa aka fara caje wadanda ake zargi kuma aka samu kudin a aljihun daya daga cikinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel