Mutane 405 Korona ta kashe a watanni biyu, Kwamitin PTF

Mutane 405 Korona ta kashe a watanni biyu, Kwamitin PTF

- Waiwayen annobar Korona ta biyu ya kwashi rayukan yan Najeriya fiye da yadda akayi tsammani

- Mambobin kwamitin PTF na ganawa da malaman addini kan rigakafin Korona

- Gwamnatin tarayya ta gano sabon nauyin cutar COVID-19 har guda bakwai a Najeriya

Mutane 405 cutar Korona ta hallaka a watanni biyu da suka gabata, kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da cutar Coronavirus ta bayyana ranar Litinin.

Hakazalika ma'aikatan kiwon lafiya 75 suka kamu da cutar makon da ya gabata, hukumar hana yaduwar cututtukan a Najeriya (NCDC) ta bayyana.

Gwamnatin tarayya ta ce an gano sabon nauyin cutar COVID-19 da ta bulla a Birtaniya har guda bakwai a Najeriya.

Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce mutane sun fi saurin mutuwa yanzu daga cutar. The Nation ta ruwaito.

A cewarsa, adadin wadanda suka mutu a daga Nuwamba zuwa yanzu ya karu mutum 405.

Boss Mustapha ya bayyana hakan ne a ganawarsa da shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) kan rigakafin cutar.

"Najeriya yanzu na fama da wani waiwaye mai saurin yaduwar gaske kamar sauran kasashen duniya, wanda ya kara adadin wadanda suka mutu daga 1,173 a 29 ga Nuwamba 2020, zuwa 1,578 a 31 ga Junairu, 2021," Mustapha ya bayyana.

"Adadin sabbin wadanda suka kamu ya kara yawa sosai."

"Ina son in bayyana cewa babu wanda ya tsira a duniyan nan sai kowa ya samu rigakafin."

KU KARANTA: Gwamna Zulum ya sallami kwamishanan lafiyan Borno, bai bayyana dalili ba

Mutane 405 Korona ta kashe a watanni biyu, Kwamitin PTF
Mutane 405 Korona ta kashe a watanni biyu, Kwamitin PTF Credit: NCDC
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamna Zulum ya sallami kwamishanan lafiyan Borno, bai bayyana dalili ba

A bangare guda, yayinda annobar korona ta yi karfi a kasar, kwamitin fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 1 ga watan Fabrairu, ta sanar da wasu jerin jihohi biyar da kananan hukumomi 22 a Najeriya da cutar COVID-19 ta yadu sosai.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, Shugaban kwamitin PTF na kasa, Dr Sani Aliyu, ya gargadi yan Najeriya a kan zuwa wadannan jihohi da abun ya shafa, jaridar Punch ta ruwaito.

A cewarsa, wadannan jihohi da kananan hukumomi da abun yayi kamari ya haifar da kaso 95 bisa dari na yawan wadanda ke kamuwa da cutar a kullun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng