Babban sarkin kabilar Yoruba ya aika muhimmin sako ga 'yan siyasa bayan ganawa da Buhari
- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da gwamnonin Jihohin Oyo da Ondo da kuma shugaban majalisar saraukan kabilar Yoruba
- Babban sarkin masarautar Ife, Adeyeye Ogunwusi, ya ce sun ziyarci Buhari ne akan al'amuran da suka shafi tsaro
- Da yake magana da manema labarai bayan ganawarsu da Buhari, Basaraken ya gargadi 'yan siyasa akan cakuda batun tsaro da siyasa
Adeyeye Ogunwusi, babban sarkin masarautar Ife ta kabilar Yoruba, ya gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, akan batun tsaro a kasa.
Da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawa da Buhari, Basaraken ya ce ziyarar tana da nasaba da al'amuran da suka shafi tsaro a yankin kudu maso yamma.
Babban sarkin ya yi kira tare da gargadin 'yan siyasa da su guji cakuda batun tsaro da siyasa tare da bayyana cewa yin hakan shine yake haddasa asarar rayuka.
KARANTA: Garkuwa da mutane: Hotunan dakarun soji mata zalla 300 da aka jibge a hanyar Abuja-Kaduna
"Shugaban kasa ya bamu tabbacin cewa ba za'a saka siyasa a sha'anin tsaro ba. Akwai balagurbin mutane a kowanne yanki na kasar nan kamar yadda muke da su a yankin kudu maso yamma.
"Na ziyarci shugaba Buhari ne a matsayina na shugaban majalisar sarakunan kabilar Yoruba domin samun tabbacinsa cewa babu wani bangare da zai saka siyasa a batun kalubalen tsaro a yankin kudu maso yamma," a cewarsa.
KARANTA: Ka daina shararawa 'yan Nigeria karya; Dan majalisa ya caccaki ministan Buhari
A baya Legit.ng ta rawaito cewa har yanzu cece-kuce bai kare ba akan hargitsin da ya afku a makon jiya tsakanin makiyayaya da 'yan kabilar Yoruba a yankin kudu maso yamma.
Sai dai, duk da shugabanni da jagororin al'umma sun tofa albarkacin bakinsu akan bahallatsar, har yanzu jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, bai ce uffan ba dangane da abubuwan ke faruwa a yankin da ya fito ba.
A cewar Cif Ayo Adebanjo, kakakin kungiyar Afenifere ta 'yan kabilar Yoruba, burin Tinubu na son yin takara a 2023 shine ya hana shi tofa albarkacin bakinsa.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng