Buhari ya bayar da dalilai hudu na kawo karshen Boko Haram a cikin shekarar nan

Buhari ya bayar da dalilai hudu na kawo karshen Boko Haram a cikin shekarar nan

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce ko kadan ba ya jin dadin yadda 'yan ta'adda ke kashe jama'a a Nigeria

- A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi wasu tsare-tsare domin kawo karshen kungiyar Boko haram a cikin shekarar 2021

- Buhari ya lissafa wasu dalilai hudu da zasu bawa gwamnatinsa damar ganin baya kungiyar Boko Haram a 2021

Biyo bayan yawaitar kai hare da salwantar rayukan 'yan kasa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana lokacin kawo karshen kungiyar Boko Haram a Nigeria.

Legit.ng ta rawaito cewa shugaba Buhari ya bayyana cewa a cikin shekarar nan, 2021, za'a kawo karshen kungiyar Boko Haram tare da neman 'yan kasa su tallafawa rundunar soji da addu'a.

Shugaba Buhari ya bayyana dalilai hudu da zasu bawa gwamnati damar kawo karshen kungiyar Boko Haram a 2021.

KARANTA: Hatsarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar yarima Nuhu, matarsa, da 'ya'yansu hudu a hanyar Abuja

1. Buhari ya bayyana cewa ko kadan ba ya kin dadin to yadda ake asarar rayuka a kasa tare da bayyana cewa nan bada dadewa ba za'a kawo karshen kungiyar Boko Haram.

2. A cewar shugaba Buhari, Nigeria za ta saka sadaukarwar jami'an soji a rai yayin yaki da 'yan ta'adda

Buhari ya bayar da dalilai hudu na kawo karshen Boko Haram a cikin shekarar nan
Buhari ya bayar da dalilai hudu na kawo karshen Boko Haram a cikin shekarar nan Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

3. Buhari ya bayyana cewa za'a kara karfafawa rundunar tsaro gwuiwa ta hanyar samar da kayan aiki da zasu basu damar murkushe 'yan ta'adda.

KARANTA: Kwastam ta gano alburusai 5,200 da aka boye cikin wasu kaya, kudinsu ya haura N378m

4. Kazalika, ya kara da cewa gwamnati Za ta kara inganta kunshin tsarin walwalar jami'an tsaron da ke yaki da 'yan ta'adda.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa duk wani mai kishin kasa a yanzu zai fi son a alakanta shi da jam'iyyar APC.

A baya Legit.ng Hausa ta rawaito cewa fadar shugaban kasa ta yi raddi tare da yi wa jam'iyyar adawa ta PDP kaca-kaca.

A wani jawabi da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya fitar, fadar shugaba kasa ta ce duk wani sauran tasiri da PDP keda shi ya kare saboda ta zama jami'ar karya, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

A cewar fafa shugaban kasa, jam'iyyar PDP ba ta yi komai ba a tsawon mulkinta na shekaru goma sha shidda bayan assasa cin hanci da rashawa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel