Shugaba Buhari ya jaddada rijistarsa matsayin mamban jam'iyyar APC (Hotuna)
Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Asabar, 30 ga watan Junairu, 2021, ya jaddada rijistarsa a matsayin mamban jam'iyyar All Progressives Congress APC a Najeriya.
Buhari ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita da yammacin nan inda yace: "Yau a Daura, na yi musharaka a shirin rijista da jaddada rijistan jam'iyyarmu mai girma APC."
Buhari tare da jigogin wasu jam'iyyun siyasar adawa a Najeriya suka hada kai aka kafa jam'iyyar APC a 6 ga Febrairu, 2013.
Jam'iyyun siyasan da sukayi hadin gambiza sun hada da Congress for Progressive Change (CPC), All Nigeria Peoples Party (ANPP), Action Congress of Nigeria (ACN) da wani ballin All Progressives Grand Alliance (APGA).
KU DUBA: EFCC ta damke wasu daliban makarantar damfara a Abuja
KU DUBA: COVID-19: Jihohi 7 a arewacin Najeriya za su mori tallafin $900,000
Jiya mun kawo muku rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari ya tashi da Abuja inda ya nufi Daura, jihar Katsina, mahaifarsa domin musharaka a sabon rijistan mambobin jam'iyyar All Progressives Congress, APC.
Buhari ya tashi daga Abuja ne bayan halartan Sallar Juma'a a Masallacin fadar shugaban kasa.
Mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bayyana cewa shugaba Buhari zai kwashe kwanaki uku a Daura kafin komawa birnin tarayya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng