Bidiyo: 'Yan bindiga sun sace hadimin dan majalisa

Bidiyo: 'Yan bindiga sun sace hadimin dan majalisa

- A ranar Talata, 26 ga watan Janairu ne wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da hadimin wani dan majalisa a jihar Imo

- Sun sace Chetachi Linus Igboebyesi wanda jama'a ke kira da London Biggy da da dare a hanyarsa ta zuwa jihar Anambra

- Sai da suka yi raga-raga da tagar motarsa kirar Mercedes ML 350 mai lamba IMHA-45 kafin su sunkuce shi su yi gaba dashi

Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da hadimin wani dan majalisa mai wakiltar Oru ta yamma dake jihar Imo, Dominic Ezerioha.

Sun yi garkuwa da Chetachi Linus Igboenyesi, wanda aka fi sani da London Biggy da misalin karfe 11:34pm na ranar Talata, 26 ga watan Janairu yayin da yake hanyar zuwa garin Uli na jihar Anambra.

A wani bidiyo da wasu ganau suka dauka, anga inda 'yan bindigan suka ragargaza tagar motar wanda suka yi garkuwa dashi kafin su sace shi su yi awon gaba.

KU KARANTA: 'Yan Najeriya sun yi wa Melaye martani bayan ya wallafa bidiyon asibitin rakuma a Dubai

Bidiyo: 'Yan bindiga sun sace hadimin dan majalisa
Bidiyo: 'Yan bindiga sun sace hadimin dan majalisa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: UGC

Igboenyesi yana cikin wata farar Mercedes ML 350 4Matic mai lamba IMHA-48 lokacin da lamarin ya faru.

Dan sandan da ya tabbatar wa da The Nation aukuwar lamarin ya ce yanzu haka 'yan sanda sun zage damtse wurin ganin sun ceto shi.

KU KARANTA: Dangote: Yadda tsohuwar budurwata ta so 'warwarar' $5m daga wurina

A wani labari na daban, kungiyoyin 'yan bindiga biyu sun yi arangama a kauyen Illela da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, lamarin da ya kawo halakar 'yan bindiga masu yawa sannan wasu suka samu miyagun raunika.

Rikicin ya barke tsakanin sansanin Mani Sarki da Dankarami da ke sansaniin Abu Rada a ranar Alhamis da ta gabata.

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa, Sarki wanda yanzu tubabben dan bindiga ne wanda ya mora rangwamen gwamnati ana kallon shi a matsayin bare a sauran sansani da ke dajikan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel