'Yan Najeriya sun yi wa Melaye martani bayan ya wallafa bidiyon asibitin rakuma a Dubai

'Yan Najeriya sun yi wa Melaye martani bayan ya wallafa bidiyon asibitin rakuma a Dubai

- 'Yan Najeriya sun yi caa kan Sanata Dino Melaye bayan ya wallafa bidiyon asibitin rakuma a Dubai

- Tsohon sanatan da ya wakilci jihar Kogi ya wallafa bidiyon ne a shafinsa na Twitter a ranar Laraba

- Amma kuma 'yan Najeriya sun yi masa kaca-kaca inda suka ce ai ya tabata rike kujerar siyasa amma babu amfani

Dino Melaye, tsohon sanatan da ya wakilci jihar Kogi ya janyo mahawara mai zafi daga 'yan Najeriya a kafar sada zumuntar zamani bayan ya wallafa bidiyon asibitin rakuma da ke Dubai.

Melaye ya wallafa bidiyon asibitin rakuman a shafinsa na kafar sada zumuntara zamani ta Twitter a ranar Laraba, 27 ga watan Janairu.

A tsokacin da yayi akasan bidiyon, ya wallafa: "Rakumi yana da asibiti a Dubai fa".

KU KARANTA: Dan Najeriya ya gina katafaren gida da robobin lemu da ruwa cike da kasa (Hotuna)

'Yan Najeriya sun yi wa Melaye martani bayan ya wallafa bidiyon asibitin rakuma a Dubai
'Yan Najeriya sun yi wa Melaye martani bayan ya wallafa bidiyon asibitin rakuma a Dubai. Hoto daga @dino_melaye, @sfl_media
Asali: Twitter

Ya ce a yayin da 'yan Najeriya ke neman asibitin dan Adam, Dubai sun wuce nan domin su har rakuma suke yi wa asibitoci.

Bidiyon kyakyawan asibitin rakuman da Melaye ya wallafa ya matukar tunzura 'yan Najeriya wanda hakan yasa suka yi caa a kanshi tare da caccakarsa.

Jama'a da dama sun koka da yadda dan Adam a Najeriya bai samu darajar samun kwatankwacin asibitin rakuma na Dubai ba.

Sun kara caccakar tsohon sanatan yadda ya kasa tabuka abun arziki ga jama'arsa a lokacin da yake wakilcinsu.

KU KARANTA: Biyu daga cikin yara 18 da aka dawo dasu daga Anambra 'yan jihar Kano ne

A wani labari na daban, NGF ta ce ba canza shugabannin tsaro ne kadai zai kawo garanbawul ba ga matsalolin tsaron da Najeriya take fuskanta, Punch ta wallafa hakan.

Wajibi ne shugaba Muhammadu Buhari ya sanya ido kuma ya dinga bai wa shugabannin tsaro umarni yadda ya dace a matsayinsa na kwamandansu.

"Babban matakin da Buhari zai dauka shine canja salo da kuma fuskantar matsalolin tsaro gadan-gadan. Sai ka ji yana cewa ya taras da tabarbarewar tsaron Najeriya a 2015 ya nunka halin da ake ciki yanzu, wannan kalaman suna matukar tayar da hankali."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel