Zamfara: 'Yan bindiga sun kai hari mazabar shugaban majalisa, sun hallaka mutane uku

Zamfara: 'Yan bindiga sun kai hari mazabar shugaban majalisa, sun hallaka mutane uku

- Wasu 'yan bindiga dadi sun kai hari garin Magarya, karamar hukumar Zurmi, jihar Zamfara

- 'Yan bindigar sun kashe mutane uku, sun sace shanu fiye da 100 tare da kone rumbunan da jama'a suka adana kayan abinci

- Garin Magarya ne mahaifar Alhaji Nasiru Muazu Magarya, shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara

Wasu 'yan bindiga dadi sun kai hari garin Magarya da ke yankin karamar hukumar Zurmi, jihar Zamfara, a ranar Talata.

Garin Magarya ne mahaifar shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara, Alhaji Nasiru Muazu Magarya.

"Wasu 'yan ta'adda dauke da muggan makamai sun dira garin Magarya tare da budewa jama'a wuta.

KARANTA: Hoton mace bakar fata zai maye gurbin na tsohon shugaban Amurka a jikin Dala

"Sun hallaka mutane biyu nan take, sun lalata dumbin dukiya tare da yin awon gaba da shanu fiye da 100 bayan sun kone rumbunan da jama'a suka adana abinci," kamar yadda wani dan majalisa ya shaidawa Daily Trust.

A ranar Laraba ne Honarabul Muazu ya jagoranci tawagar jami'an gwamnati zuwa garin Magarya domin jajantawa jama'a akan abinda ya faru.

Zamfara: 'Yan bindiga sun kai hari mazabar shugaban majalisa, sun hallaka mutane uku
Zamfara: 'Yan bindiga sun kai hari mazabar shugaban majalisa, sun hallaka mutane uku
Source: Twitter

Dagacin Magarya ya zagaya da tawagar jami'an domin su ganewa idanuwansu irin barnar da 'yan bindiga suka tafka a garin.

KARANTA: Afenifere ta bayyana dalilin da yasa Tinubu yake tsoron tunkarar Buhari a kan bahallatsar makiyaya da Yoruba

A yayin da yake gabatar da jawabin jaje, Honarabul Muazu ya dauki alkawarin za'a turo karin jami'an tsaro zuwa yankin domin zakulo 'yan ta'adda.

A kwanakin baya Legit.ng ta rawaito shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na cewa ko kadan ba ya jin dadin yadda 'yan ta'adda ke salwantar da rayukan jama'a a sassan Nigeria.

A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi wasu tsare-tsare domin kawo karshen kungiyar Boko haram a cikin shekarar 2021.

Buhari ya lissafa wasu jiga-jigan dalilai guda hudu da zasu bawa gwamnatinsa damar ganin bayan kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin wannan shekarar, 2021.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel