Wata cuta ta bulla a Sokoto, ta kashe mutum 4, wasu 24 su na jinya a asibiti

Wata cuta ta bulla a Sokoto, ta kashe mutum 4, wasu 24 su na jinya a asibiti

- Gwamnati ta tabbatar da bayyanar wata cuta da ba a iya gane kanta ba a Sokoto

- Gwamnan jihar Sokoto ya ce wannan cuta ta ci mutane 4, yayin da 24 su ke jinya

- Aminu Tambuwal ya fitar da jawabi, ya ce gwamnati za ta binciki wannan annoba

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa mutane su na mutuwa a asibiti a sakamakon bullar wata bakuwar cuta yankin Helele da ke jihar Sokoto.

Mai girma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar da bayyanar wannan annoba, a wani jawabi da ya fitar da kansa a ranar Talata.

Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa mutane 24 su na kwance a gadon asibiti, su na jinyar wannan sabuwar cuta a asibitocin jihar Sokoto.

Gwamnan ya ce an kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike a game da wannan cuta domin gano asalinta da kuma magungunan da zasu warkar da ciwo.

KU KARANTA: Gwamonin da su ka kamu da COVID-19 a Najeriya

A jawabin gwamnan, ya nuna takaicinsa game da wannan annoba, ya yi ta'ziyya ga iyalan wadanda suka rasa ‘yanuwansu a garin Helele a dalilin cutar.

“Ya zo gare mu cewa wata sabuwar cuta ta ci mutane hudu, uku a cikin yankin Helele, daya kuma yayin da yake kwance a gadon asibiti.” Inji Aminu Tambuwal.

Jawabin ya ce: “Mutane 24 suna kwance yanzu haka ana duba su a asibitoci dabam-dabam da ke Sokoto.”

Kamar yadda gwamnan ya bayyana a yau, kwamishonin harkar kiwon lafiya da na muhalli ne za su jagoranci kwamitin da zai yi bincike a game da wannan cuta.

KU KARANTA: Bill Gates ya ba Buhari shawara a kan sayen magungunan COVID-19

Wata cuta ta bulla a Sokoto, ta kashe mutum 4, wasu 24 su na jinya a asibiti
Gwamna Aminu Tambuwal Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce: “Bugu da kari, gwamnati ta dauki dawainiyar kula da mutanen da ke jinya a sakamakon wannan cuta, ta na yi masu fatan samun sauki, su koma ga iyalansu.”

Dazu kun ji cewa annobar cutar COVID-19 ta kashe mutane fiye da 1500 a Najeriya. Alkaluman da hukumar NCDC suka fitar ya tabbatar da wannan mummunan lamari.

A dalilin haka ne gwamnatin tarayya ta bada umarni a jiya cewa duk ma’aikatan da su ke mataki na 12 zuwa abin da ya yi kasa, su cigaba aiki daga dakunan gidajensu.

Coronavirus ta sa gwamnati ta tsawaita umarnin da aka ba ma’aikata game da zuwa ofis.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel