Yaki da rashawa: Jami’an EFCC sun yi ram da tsohon dan takarar shugaban kasa, Turaki

Yaki da rashawa: Jami’an EFCC sun yi ram da tsohon dan takarar shugaban kasa, Turaki

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, sun kai ma tsohon minista a gwamnatin Jonathan, tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Kabiru Tanimu Turaki.

Legit.ng ta ruwaito Kabiru Tanimu Turaki shine tsohon ministan ayyuka na musamman a gwamnatin Gooluck Jonathan, kuma mataimakin shugaban yakin neman zaben Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, mai kula da al’amuran mulki.

KU KARANTA; Murnar samun nasarar Buhari: Matashi ya fara tattaki daga Legas zuwa Abuja

Yaki da rashawa: Jami’an EFCC sun yi ram da tsohon dan takarar shugaban kasa, Turaki
Turaki
Asali: UGC

Kaakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ne ya tabbatar da EFCC ta kama Kabiru cikin wata sanarwa daya fitar a tsakar daren Litinin, inda yace hukumar ta gayyaci Kabiru ne a ranar Litinin, inda ya amsa gayyatar da tayi masa.

Sai dai daga zuwa ofishinnasu sai suka kamashi, sa’annan suka sakayashi tare da cigaba da rikeshi ba tare da wani kwakkwara dalili ba, don haka kaakaki Kola yace suna kira ga EFCC data gaggauta sakinsa ba tare da wani sharadi ba.

Bugu da kari PDP tayi zargin kama tsohon Ministan na daga cikin manakisar da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da jam’iyyar APC suke shirya ma jam’iyyar PDP da sauran abokan hamayya domin su lalata duk wani shiri da suke yin a kwatar mulki a gaban kotu.

“Tun bayan da Atiku Abubakar tare da jam’iyyar PDP muka yanke shawarar garzaya gaban kotu don kwatar mulkin da aka kwace mana da karfin tuwo, sakamakon muna da hujjoji, an yi ta cin zarafin shuwagabanninmu tare da yin barazana da kuma bamu baki don mu fasa zuwa kotu.

“An kama Tanimu Turaki ne a lokacin da EFCC ta gayyaceshi don ya tsaya a matsayin wanda zai samar da beli ga surukin Atiku Abubakar, kuma daraktan kudi na kamfanin Atiku, Babalele Abdullahi, wanda EFCC ta kama a kwanakin baya.” Inji shi.

Daga karshe kaakakin yace babu wani barazana da gwamnatin APC zata musu da zai sa su fasa zuwa gaban kotu don kwatar mulkin da yan Najeriya suka baiwa Atiku Abubakar amma aka danne masa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel