Afenifere ta bayyana dalilin da yasa Tinubu yake tsoron tunkarar Buhari a kan bahallatsar makiyaya da Yoruba

Afenifere ta bayyana dalilin da yasa Tinubu yake tsoron tunkarar Buhari a kan bahallatsar makiyaya da Yoruba

- Akwai jita jitar cewa akwai siyasa a rikicin da ya barke a yankin kudu maso yamma a tsakanin makiyayaya da Yarabawa

- Tuni aka fara zargin cewa jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi gum akan batun saboda burinsa na son yin takara

- Ayo Adebanjo, kakakin kungiyar Afenifere, ya ce ya ki yin magana ne saboda yana goyon bayan mutanen arewa

Har yanzu cece-kuce bai kare ba akan hargitsin da ya afku a makon jiya tsakanin makiyayaya da 'yan kabilar Yoruba a yankin kudu maso yamma.

Sai dai, duk da shugabanni da jagororin al'umma sun tofa albarkacin bakinsu akan bahallatsar, har yanzu jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, bai ce uffan ba, kamar yadda Punch ta rawaito.

A cewar Cif Ayo Adebanjo, kakakin kungiyar Afenifere ta 'yan kabilar Yoruba, burin Tinubu na son yin takara a 2023 shine ya hana shi tofa albarkacin bakinsa.

DUBA WANNAN: NDLEA: Marwa zai farfado da tsohon atisaye domin yaki da kwaya a Nigeria

Cif Adebanjo ya bayyana cewa tsammanin samun goyon bayan arewa a zabe mai zuwa ya hana Tinubu yin magana saboda yana tsoron duk wani abu da zai fusata arewa.

Afenifere ta bayyana dalilin da yasa Tinubu yake tsoron tunkarar Buhari a kan bahallatsar makiyaya da Yoruba
Afenifere ta bayyana dalilin da yasa Tinubu yake tsoron tunkarar Buhari a kan bahallatsar makiyaya da Yoruba
Asali: UGC

Kakakin ya kara da cewa Tinubu ba zai iya tunkarar Buhari akan batun makiyayaya ba saboda yana tsammanin cewa zai goya masa baya wajen samun tikitin takarar shugaban kasa a jami'yyar APC.

DUBA WANNAN: Dumbin masu zanga-zangar ENDSARS sun dawo suna 'kwantar da kai' akan aikin dan sanda

A kwanakin baya Legit.ng ta rawaito shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na cewa ko kadan ba ya jin dadin yadda 'yan ta'adda ke salwantar da rayukan jama'a a sassan Nigeria.

A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi wasu tsare-tsare domin kawo karshen kungiyar Boko haram a cikin shekarar 2021.

Buhari ya lissafa wasu jiga-jigan dalilai guda hudu da zasu bawa gwamnatinsa damar ganin bayan kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin wannan shekarar, 2021.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel