Hausawa mutanen kirki ne, Fulani ne matsalan Najeriya: Nnamdi Kanu
- Karon farko, Nnamdi Kanu ya sassauta murya kan mutan Arewa
- Kanu ya ce yana matukar ganin girman Hausawa kuma yana son su
Shugaban haramtacciyar kungiyar masu yakin kafa kasar Biyafara, Nnamdu Kanu, ya ce Hausawa na nuna halayen kirki wajen alaka da yan kabilar Igbo.
Amma ya ce mutanen Fulani ne suka kasance matsala ga Inyamurai da sauran kabilun Najeriya.
Kanu ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ta mai magana da yawunsa, Emma Powerful.
A cewarsa, Fulani na son shafawa Hausawa kashin matsalan da suka haifarwa Najeriya ta hanyar kiran kansu 'Hausa-Fulani'.
Kanu ya yi kira ga Hausawa kada su bari wani ya jefasu cikin matsalar da Fulani suka haifar.
Yace: "Tun 2015 muna jin Fulani kaza, Fulani kaza, amma saboda wutan da IPOB ta kunna musu, sun fara amfani da sunan Hausa-Fulani domin boye halinsu saboda Hausawa mutanen kirki ne."
"Ina son in bayyana cewa mu yan Biyafara bamu da matsala da Hausawa. Ina ganin girman Hausawa kuma ina son su. Hausawa mutanen kirki ne."
"Shi yasa mu yan Biyafara muka zabi Bahaushe ma matsayin kansila sau biyu a Enugu."
Matsalar Najeriya Fulani ce..Abinda ke hana Fulani Makiyaya kwace Najeriya kungiyar IPOB ce."
KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta fara rabawa mata N20,000 a jihar Kaduna
KU KARANTA: NIMC ta bai wa MTN, Airtel, da sauran wasu kungiyoyi lasisin yin NIN
A bangare guda, har yanzu cece-kuce bai kare ba akan hargitsin da ya afku a makon jiya tsakanin makiyayaya da 'yan kabilar Yoruba a yankin kudu maso yamma.
Sai dai, duk da shugabanni da jagororin al'umma sun tofa albarkacin bakinsu akan bahallatsar, har yanzu jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, bai ce uffan ba, kamar yadda Punch ta rawaito.
A cewar Cif Ayo Adebanjo, kakakin kungiyar Afenifere ta 'yan kabilar Yoruba, burin Tinubu na son yin takara a 2023 shine ya hana shi tofa albarkacin bakinsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng